Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mitoma zai yi jinya har zuwa ƙarshen kakar wasa
Dan wasan Brighton Kaoru Mitoma ba zai buga sauran wasannin kakar bana ba sakamakon rauni da ya ke fama da shi.
Matsalar ce ta hana ɗan wasan na Japan buga wasan da Brighton ta yi kunnen doki da Everton.
"Babbar matsala ce. Ina tsammanin zai kai watanni biyu ko uku, [don haka] kakar wasansa ta ƙare kenan," in ji De Zerbi kafin wasan cin kofin FA da za su buga ranar Laraba da Wolves.
"Rauni ne ya ji a baya wanda ya hana shi buga karawar da Everton."
Bayan taka rawar gani a kakar wasan da ta gabata a Seagulls yayin da suka cancanci shiga Gasar Europa a karon farko, wanna kakar ba ta yi wa Mitoma kyau ba saboda raunuka da ya yi fama da su.
A ƙarshen shekarar 2023, ya samu rauni a idon sawunsa wanda hakan ya sa bai taka leda ba na tsawon wata guda, wanda hakan ya hana shi buga akasarin wasannin Japan a gasar cin kofin nahiyar Asiya.
Ya kuma koma taka leda a wasanni biyu na ƙarshe kafin Iran ta fitar da Japan a zagayen kusa da na ƙarshe.
De Zerbi ya tabbatar da cewa ƴan wasan gaba Evan Ferguson da Joao Pedro ba za su buga wasan zagaye na biyar na gasar cin kofin FA a Molineux ba yayin da ɗan wasan baya Joel Veltman da ɗan wasan gaba Danny Welbeck za su yi gwajin lafiyar jiki kafin wasansu na gaba.