Kungiyoyin agaji na waje sun dakatar da aiki bayan Taliban ta hana mata aiki da su

Asalin hoton, EPA
Manyan kungiyoyi masu zaman kansu na kasashen waje uku sun dakatar da ayyukansu a Afghanistan bayan Taliban ta haramta wa mata yi musu aiki.
A wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar, kungiyar Care International, da ƙungiyar agaji mai zaman kanta ta ƙasar Norway (NRC), da kuma Save the Children sun ce ba za su iya ci gaba da ayyukansu ba "ba tare da ma'aikatanmu mata ba."
Kungiyoyin agajin sun kuma "bukaci" a bar mata su ci gaba da yi musu aiki.
Shugabannin Taliban da ke mulki a Afghanistan na ci gaba da abin da ake ganin tauye hakkin mata ne.
Matakin kungiyoyin ya zo ne 'yan kwanaki bayan Taliban ta haramta wa mata zuwa jami'oi.
Abdel Rahman Habib, mai magana da yawun ma'aikatar tattalin arziki ta Taliban, ya yi ikirarin cewa matan da ke aiki da kungiyoyin sun karya dokar shigar da ya kamata su yi na sanya hijabi.
Kungiyar Taliban ta yi barazanar soke lasisin duk kungiyar da ba ta yi aiki da hanin da suka yi ba nan take.
Shugabannin Care da na NRC da kuma Save the Children sun ce kungiyoyinsu "ba su iya kaiwa ga miliyoyin al'ummar Afghanistan da ke bukatar taimako ba tun daga watan Agustan 2021" ba tare da mata ma'aikatansu ba.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"Yayin da muke dakon karin haske kan wannan haramcin, mun dakatar da ayyukanmu, mun kuma bukaci cewa mata da maza suna da damar da za su ci gaba da tallafawa don ceto rayukan mutanen Afghanistan," kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Ramiz Alakbarov, wani babban jam'in kula da agaji na Majlisar Dinkin Duniya (MDD) ya ce majalisar na kokarin ganin an cire haramcin wanda "ke barazana ga baki daya al'umomin da ke bukatar agaji".
MDD za ta iya dakatar da kai kayan agaji baki daya zuwa Afghanistan idan hukumomin Taliban ba su soke haramcin da suka yi wa mata na aikin gajin ba, kamar yadda jami'in ya shaida wa BBC.
Amma Mista Alakbarov ya ce kawo yanzu ba a san karara me Taliban ke nufi ba da wannan umarni.
Ya ce ministan ilimi na Taliban ya shaida wa MDD cewa hukumar za ta iya ci gaba da ayyukanta da suka shafi kiwon lafiya kuma mata za su iya "zuwa su aiwatar da ayyukansu".
Wasu ma'aikatun ma sun tuntubi MDD, inda suka ce za a iya ci gaba da tallafin da ake bayarwa ta fuskar bala'o'i da ayyukan ko-ta-kwana, a cewarsa.
Jan Egeland na kungiyar NRC ya ce kusan ma'aikata 500 cikin ma'aikata 1,400 da ke aiki da kungiyar mata ne.
Haka kuma ma'aikata matan na yin aiki "tare da kare dukkanin abin da suka shafi al'adu da dokokin sanya tufafi da yadda suke zirga-zirga da kuma raba ofisoshi".
Ya ce yana fatan za a janye umarnin "cikin 'yan kwanaki masu zuwa" inda ya yi gargadin cewa miliyoyin mutane za su ji jiki idan kungiyoyin agaji suka samu tsaiko a ayyukansu".
Kungiyoyin masu zaman kansu sun kuma nuna damuwarsu kan tasirin da hanin zai yi a kan ayyukan yi a yayin da ake cikin matsalar tattalin arziki sosai.
Matan Afghanistan da ke aiki da kungiyoyin na tallafa wa iyalansu, a baya sun bayyana wa BBC fargabarsu na rashin yadda za su yi saboda dokar.
Daya daga cikinsu ta ce: "idan ban je na yi aiki ba, wane ne zai taimaka wa iyali na?"
Wata kuma ta bayyana yadda ta ji labariin da cewa "ya kada ta" inda ta jaddada cewa tana bin ka'idojin sanya sutura kamar yadda Taliban ta ce a yi.
Hanin ya janyo korafi daga kasashen duniya.
Ministan Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya yi gargadin cewa hakan zai kawo "matukar tsaiko ga ceton rayukan miliyoyin mutane mabukata."
A shekarar 2021 ne kungiyar ta Taliban ta sake karbe iko da Afghanistan shekara 20 bayan dakarun kawance da Amurka ke jagoranta sun tunbuke su daga mulki.











