Man United na son dauko Bellingham, da mai tsaron ragar Switzerland Yann

Bellingham

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Manchester United ta shiga gudun yada kanin wani, domin sayo dan wasan tsakiya na Ingila Jude Bellingham, mai shekara 19, daga Borussia Dortmund.

Su ma kungiyoyin Liverpool da Manchester City da Real Madrid na daga cikin kungiyoyin da ke zawarcin dan wasan. (Sky Sports Germany)

Real Madrid ba za ta biya sama da yuro miliyan 125 domin sayo Bellingham daga kulub din Jamus ba. (Defensa Central - in Spanish)

Zai yi wuya Inter Milan ta kauda kai kan yarjejeniyar yuro miliyan 50, da wata yuro miliyan 10 a gefe, za dai a sayo mai tsaron gid ana Denmark Denzel Dumfries, mai shekara 26, d ake rade-radin ya na da laka da kungiyoyin Chelsea da Manchester United.(Calciomercato - in Italian)

Manchester United ta fara tattaunawa kan aniyar dauko mai tsaron ragar Switzerland Yann Sommer, mai shekara 33, wanda kwantiraginsa da Borussia Monchengladbach zai kare a karshen kakar nan. (Bild, via Mirror)

Dan wasan Atletico Madrid da Slovenia Jan Oblak, mai shekara 29, na daga cikin wadanda Manchester United ke duba yiwuwar sayowa a matsayin sabon mai tsaron raga. (Fichajes - in Spanish)

West Ham na son dauko dan wasan tsakiya na Brazil Luizao kan kwantiragin shekaru uku da rabi da zarar dan wasan mai shekara 20 ya gama da kwantiraginsa na Sao Paulo a karshen watan Junairun badi. (90 Min)

An bai wa ‘yan wasan Ingila shawarar su yi taka tsantsan da daukar matakan kariya da tsaron lafiyarsu, bayan wasu barayi sun afka gidan dan wasan Chelsea winger Raheem Sterling ana tsaka da gasar cin kofin duniya a Qatar, lamarin da ya sanya shi komawa gida babu shiri.(Times)

Leeds United ba ta yanke shawarar kammala kwantiragin dauko dan wasan gaba na Sifaniya Rodrigo, mai shekara 31, ya yin da kwantiraginsa ke karewa nan da watanni 18 masu zuwa. (Leeds Live)

Napoli na bi wasu takwarorinta domin zawarcin dan wasan tsakiya na Ivory Coast  Franck Kessie mai shekara 25, wanda burin sa shi ne ci gaba da zama a kungiyar Barcelona.(Relevo - in Spanish)

Kociyan Burnley Vincent Kompany na daga cikin wadanda ake kyautata zaton zai maye gurbin dan wasan Belgium Roberto Martinez a matsayin kociyan kungiyar. (Sun)