Sergio Aguero ya yi atisaye a Barcelona ranar Laraba

Sergio Aguero

Asalin hoton, Barcelona FC

Bayanan hoto, Sergio Aguero shine kan gaba a yawan ci wa Manchester City kwallaye a tarihi
An wallafa

Kwanan nan Barcelona za ta fara cin moriyar Sergio Aguero, bayan da ya fara atisaye ranar Laraba.

Aguero ya koma Barcelona da taka leda a bana, bayan da kwantiraginsa ya kare a Manchester City a karshen kakar bara.

Mai shekara 33, wanda ya bayar da gudunmuwar da Argentina ta lashe Copa America a bana, ya ji rauni tun kan fara wasannin kakar bana.

Barcelona wadda ke fuskantar kalubale a bana za ta yi murna da zarar dan kwallon ya fara buga mata tamaula.

Kungiyar Camp Nou tana ta shida a teburin La Liga, bayan da abokiyar hamayyarta, Atletico Madrid ta doke ta 2-0 - ta kuma sha kashi a wasa biyu na cikin rukuni a Champions League a bana.

Aguero ya murmure wanda a ranar Laraba ya buga atisaye a karawar sada zumunta da UE Cornella.

Yanzu dai ba a fayyace ko dan kwallon tawagar Argentina zai buga wa Barcelona gasar La Liga da za ta fafata da Valencia ranar Lahadi ba.

Daga nan ta fuuskanci Dynamo Kiev a Champions League, sai karawar hamayya ta El Clasico da Real Madrid za ta ziyarci Camp Nou ranar 24 ga watan Oktoba.