Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Bellingham, Rudiger, Pepi, Haidara, Salah, Dybala, da Torres

Asalin hoton, Getty Images
Liverpool na kan gaba a jerin kungiyoyin da ke son daukar Jude Bellingham, dan wasan tsakiya mai shekara 18, dan asalin Ingila daga Borussia Dortmund a kakar wasa mai zuwa. (Mirror)
Real Madrid ne ke kan gaba wajen raba Antonio Rudiger, dan wasa mai shekara 28 domin kwantiraginsa ta kusa karewa da Chelsea. (Independent)
Manchester United da Liverpool na fuskantar turjiya daga Atletico Madrid kan Ricardo Pepi, dan wasan gaba dan asalin Amurka mai shekara 18. (Mirror)
Dan wasan da sabon kocin Manchester United Ralf Rangnick ya fi so a yanzu shi ne Amadou Haidara na RB Leipzig. Dan wasan tsakiya mai shekara 23dan kasar Mali ne. (Mirror)
Kocin Liverpool Jurgen Klopp ya ce babu wata damuwa kan halin da Mohamed Salah dan wasan gaba mai shekara 29 ke ciki dangane da sabuwar kwantiraginsa. (Guardian)
Har wa yau dai Liverpool ta bayyana sha'awarta ta dauko Paulo Dybala, dan wasan gaba na Argentina daga Juventus da zarar kwantiraginsa ta kare a karshen kakar wasan nan. (Calciomercato - in Italian)
Ajax na duba yiwuwar daukar golan Manchester United Dean Henderson mai shekara 24, a matsayin dan wasa na aro. Kungiyar na kuma son dauko Steven Bergwijn, dan wasa mai shekara 24 dan kasar Holland daga Tottenham. (MEN)





