Johann Rupert ya zarce Ɗangote a matsayin mutum mafi arziƙi a Afirka

..

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Johann Rupert controls several global luxury brands and also has major investments in South Africa
    • Marubuci, Wycliffe Muia
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 3

Attajirin nan ɗan ƙasar Afirka ta Kudu, Johann Rupert ya zarce attajirin nan ɗan Najeriya, Aliko Ɗangote a matsayin wanda ya fi kowa arziƙi a nahiyar Afirka, kamar yadda mujallar Bloomberg Billionaires Index.

Mista Rupert shi ne mai kamfanin Richemont wanda ɗaya ne daga cikin manyan kamfanonin da ke samar da kayan alatu da suka haɗa da shagunan Cartier and Montblack da ke sayar da turaren da agoguna da sauransu.

Yawan kuɗin attajirin sun ƙaru zuwa dala biliyan 14.3 daga dala biliyan 1.9, abin ya sa ya zama mai kuɗin duniya na 147 inda ya bai wa Ɗangote na Najeriya tazarar mutum 12.

Arziƙin Ɗangote dai ya ragu ne da dala biliyan ɗaya da miliyan ɗari bakwai ($1.7bn) a shekarar nan ta 2024, abin da ya mayar da yawan dukiyarsa zuwa dala biliyan 13.4, in ji mujallar Bloomberg.

Dalilan da suka sa Johann ya ƙwace kambu daga hannun Ɗangote

Naƙasun da dukiyar Ɗangote ta samu na nuni da irin tawayar da tattalin arziƙin Najeriya ya samu, inda mafi yawancin kamfanoninsa suke.

Tun dai bayan hawan shugaba Bola Tinubu a bara, gwamnatinsa ta bullo da tsare-tsaren tattalin arziƙi a ƙasar mafi yawan jama'a a nahiyar Afirka da suka haɗa da cire tallafin man fetur wanda ya ta'zzara hauhawar farashin kayayyaki wanda yanzu haka ta kai kaso 30 cikin ɗari.

Shugaba Tinubu dai ya ce tsare-tsaren sun zama dole ne domin rage kashe kuɗaɗen gwamnati ta hanyar sauya akalarsu zuwa cigaban ƙasa a nan gaba.

Faɗuwar darajar naira ta shafi Aliko ɗangote wanda mafi yawancin arziƙinsa yana ta'alaka ne da kadarorin da daraja ko akasin naira ke fayyace ƙimarsu.

Ɗangote mai shekara 66, ya samu arziƙin nasa ne a harkar sukari da siminti inda kuma a bara ya kafa matatar mai a birnin Legas.

A ƴan watannin nan rukunin kamfanoninsa mai suna Ɗangote Group sun fuskanci ƴan matsaloli sakamakon tsaiko a sabuwar matatar man nasa.

A watan janairun nan ne dai mujallar Forbes ta wallafa sunansa a matsayin wanda ya riƙe kambun mafi arziƙi a nahiyar Afirka a karo na 13 a jere duk da komabayan tattalin arziƙin da ƙasarsa ta fuskanta.

To sai dai yanzu rahoton da mujallar Bloomberg ta fitar, ya ayyana Ɗangoten a matsayin mai arziƙin nahiyar Afirka na biyu sannan kuma na 159 a duniya.

Wane ne Johann Rupert?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ƙaruwar arziƙin na mista Rupert ya samu tagomashi ne a sana'ar kayan alatu.

Kamfanonin da mista Rupert ke jagonta baya ga kamfanin Richemont da ke ƙasar Switzerland, sauran kamfanonin nasa sun haɗa da Remgro wani kamfanin ababan hawa a Afirka ta Kudu da ke da hannayen jari a kamfanoni fiye da 30, kamar yadda mujallar ta Bloomberg ta rawaito.

Mista Rupert ya kuma gaji dukiya daga mahaifinsa, Anton Rupert wanda ɗan kasuwa ne da ya fara daga harkar taba inda kuma ya zamo babban attajiri a fagen kayan alatu.

Attajirin ɗan ƙasar Afirka ta Kudu ya halarci jami'ar Stellenbosch inda ya karanci ilimin tattalin arziƙi to amma daga bisani sai ya bar karatun ya shiga sana'ar mahaifinsa a shekarar 1984.

Mista Rupert ya kasance mai saka baki a harkokin siyasa da muhalli a Afirka ta Kudu sannan yana gangamin yaƙar aƙidar ƙasƙanta farar fata a madafun iko. Ya kuma samu lambobin yabo da karramawa iri-iri a harkokin kasuwancinsa.

A yanzu haka shi wannan attajirin ɗan Afirka ta Kudu na zaune ne a birnin Cape Town a wani gidan ƙasaita sannan yana da wasu ƙarin gidajen a biranen Geneva da London.

Nicky Oppenheimer, wanda shi ma ɗan Afirka ta Kudun ne shi ne mutum na uku da ke biyewa Ɗangote a masu kuɗin nahiyar Afirka, inda aka ƙimanta yawan dukiyarsa a kan dala biliyan 11.3.

Sai kuma Nassef Sawiris ɗan ƙasar Masar ne ke biye masa da arziƙi mai yawan dala biliyan 9.48. Sai kuma Natie Kirsh shi ma ɗan Afirka ta Kudu da ya zama na biyar a masu kuɗin Afirka inda yake da arziki mai yawan dalar Amurka biliyan 9.22.

Kamar dai mujallar Forbe, ita ma Bloomberg tana amfani da sauye-sauyen da ake samu a hawa da saukar dukiyar attajirai lokaci zuwa lokaci.

Kambun mutumin da ya fi kowa arziƙi na Afirka ka iya ci gaba da sauyawa a tsakanin attajiran bisa la'akari da yadda kasuwa ke jujjuyawa.