Gündoğan zai bar Barca, Chelsea za ta bayar da Sterling ta ƙarbi Chiesa

Asalin hoton, Getty Images
An cire Joe Gomez daga 'yan wasan Liverpool da suka yi nasara a karawar da suka yi da Ipswich a ranar Asabar yayin da dan wasan mai shekara 27 ke nazarin sauya wuri inda Newcastle da Aston Villa da Fulham da kuma Chelsea dukaninsu a baya sun nuna sha’awar sayan dan wasan Ingila mai tsaron baya. (Times - subscription required), external
To sai dai Liverpool ba ta nuna alamun ta na son ta cefanar da shi ba kuma kocin kungiyar Arne Slot a shirye ya ke ya sake ba dan wasan wata dama . (Liverpool Echo), external
Kocin Fenerbahce Jose Mourinho zai tuntubi tsohuwar kungiyarsa ta Tottenham domin sayan dan wasan tsakiyar Argentina Giovani lo Celso mai shekara 28 . (Express), external
Su ma Aston Villa da Roma da kuma Real Betis na sha’awar Lo Celso wanda aka fadawa cewa ba ya cikin ‘yan wasan da kocin Tottenham Ange Postecoglou ya ke son ya rike kuma zai iya barin kungiyar akan fam miliyan 13. (Fichajes - in Spanish), external
Dan wasan tsakiyar Jamus Ilkay Gundogan, mai shekara 33, ya fadawa jami’an Barcelona cewa ya na son ya bar kungiyar bayan fiye da shekara guda da ya fara taka leda a kungiyar daga Manchester City . (Sport - in Spanish), external
Wolves za ta fafata da Fenerbahce da Sevilla da kuma Marseille wajan ganin an bata aron dan wasa Sfaniya da Barcelona Ansu Fati mai shekara 21(Sport - in Spanish), external
Watakila dan wasan Ingila mai kai hari Dominic Calvert-Lewin mai shekara 27, ya bar Everton kafin a rufe kasuwar cefanar da 'yan wasa saboda kocin Toffees Sean Dyche na son ya dauko wani dan wasa da kuma dan wasan tsakiya da dan wasa mai hari . (Football Insider), external
Manchester City ta fara shirin yi wa dan wasan tsakiya na Sfaniya Rodri tayin karin albashin fam dubu 370 a kowane mako domin dan wasan mai shekara 28 ya ci gaba da taka mata leda . (Sunday Mirror), external
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Mai tsaron ragar Georgia, Giorgi Mamardashvili, mai shekara 23, na son ya koma Liverpool kuma kungiyarsa ta yanzu Valencia ta amnce masa barin kulob din idan sun sami wanda zai maye gurbinsa. (Football Espana), external
Manchester United na son ta riga Liverpool wajan sayan Mamardashvili, sai dai ta na bukatar ta rage yawan ‘yan wasanta tare da neman karin kudi ta hanyar sayar da dan wasa mai kai hari na Ingila Jadon Sancho, mai shekra 24. (Mirror), external
Watakila dan wasa mai tsaron baya na Poland Jakub Kiwior ya bar Arsenal kafin kasuwar sayar da ‘yan wasa ta zo karshe ko da yake ba bu wata yarjejeniyar da aka cimma da dan wasan mai shekara 24 . (Fabrizio Romano), external
Bayern Munich a shirye take ta saurari tayin da aka yi wa dan wasan tsakiyarta Leon Goretzka duk da cewa dan wasan kasar Jamus mai shekara 29 na son ya tsaya . (Florian Plettenberg), external
Chelsea ta yi yunkurin sayan dan wasa gaban Italiya Federico Chiesa, mai shekara 26, daga Juventus a yarjejeniyar musayar dan wasan da Raheem Sterling, mai shekara 29, sai dai yarjejeniyar ta ruguje saboda albashin dan wasa mai kai hari na Ingila . (Gianluca Di Marzio), external
Dan wasa mai kai hari na Watford da kuma Colombia Yaser Asprilla mai shekara 20, ba zai koma kungiyar Girona ba , ayin da Porto na son ta daukar sa. (Sport - in Spanish), external










