Lopetegui ya fara da rashin nasara a Premier duk da ɗinbin cefane

Julen Lopetegui

Asalin hoton, PA Media

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Aston Villa ta je ta doke West Ham United 2-1 a wasan makon farko a Premier League ranar Asabar kakar 2024/25.

Karon farko da sabon koci, Julen Lopetegui ya ja ragamar West Ham a bana, bayan maye gurbin David Moyes a kakar da ta wuce.

A minti na huɗu da fara wasa ne Aston Villa ta fara zura ƙwallo a raga ta hannun Amadou Onana.

Ya zama na uku ɗan Belgium da ya ci ƙwallo a wasansa na farko a Premier League a Aston Villa, bayan bajintar Luc Nilis a1-1 da Chelsea ranar 27 ga watan Agustan 2000) da Christian Benteke a nasarar 2-0 a kan Swansea ranar 15 ga watan Satumba 2012.

West Ham ta farke tun kan hutu a bugun fenariti ta hannun Lucas Paqueta, wanda ya buga ƙwallon ta yi gefe, mai tsaron raga, Emiliano Martinez ya faɗi ɗaya gefen.

Matty Cash ne ya jawo wa Aston Villa fenaritin, kuma karo na shida yake haddasa bugun daga kai sai mai tsaron raga tun bayan da ya fara wasa a Satumbar 2020.

Daga baya ne Aston Villa ta kara na biyu ta hannun Jhon Duran, wanda West Ham ta yi zawarcisa, amma ƙungiyar Villa Park ba ta sallamar ba.

Wannan shi ne karo na huɗu a gida a bayan nan da ake cin West Ham a wasan makon farko da fara kakar Premier League.

Lopegui tsohon kociyan tawagar Sifaniya da Real Madrid ya horar da Wolves daga baya ya ajiye aikin, bayan da ƙungiyar ke fama da matsin tattalin arziki.

Kociyan ya horar da Wolves a kakar 2022/23 a lokacin da ƙungiyar ke shirin faɗuwa daga Premier League, wanda ya tserar da ita.

Waɗanda West Ham ta ɗauka a bana kawo yanzu

  • Max Kilman daga Wolverhampton Wanderers
  • Crysencio Summerville daga Leeds United
  • Niclas Füllkrug daga Borussia Dortmund
  • Luis Guilherme daga Palmeiras
  • Aaron Wan-Bissaka daga Manchester United
  • Guido Rodríguez daga Real Betis
  • Wes Foderingham daga Sheffield United
  • Jean-Clair Todibo daga Nice
  • Saïd Benrahma daga Olympique Lyon
  • Thilo Kehrer daga Monaco