KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 15/08/2026

Wannan shafi ne da ke kawo abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar 15 ga watan Agustan 2026

Taƙaitattu

Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • xxx
  • Khalifa Dokaji
  • Sheikh Jingir
  • Kano
  • Seriki Abbas
  • xxx
  • xxx
  • Bola Tinubu
  • Senator Gaya
  • xxx
  • xxx
  • Zahra Buhari
  • xxx
  • Nigeria
  • xxx

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Isiyaku Muhammed

  1. Sojoji sun daƙile harin ISWAP a wani sansanin soji a Borno

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta na Operation Hadin Kai sun yi nasarar daƙile wani harin da mayaƙan ISWAP suka kai sansanin sojin Fo (FOB) da ke Mandaragirau a ƙaramar hukumar Biu ta jihar Borno da sanyin safiyar Juma'a.

    A wata sanarwa, rundunar ta ce mayaƙan sun kai harin ne da misalin ƙarfe 2:00 na dare ta hanyoyi biyu, amma tsarin sa ido da gargaɗi na sansanin ya gano motsinsu tun da wuri.

    Hakan ya bai wa sojoji damar tura dakaru da suka tare su, lamarin da ya janyo musayar wuta mai zafi.

    Sanarwar ta ƙara da cewa mayaƙan da suka yi ƙoƙarin kutsawa cikin sansanin ta wata hanya ta daban sun gamu da turjiya mai ƙarfi, wanda ya tilasta musu janyewa.

    Daga bisani sojojin sun bi sawunsu tare ƙwace makamai da sauran kayan aiki.

    Rundunar ta ce an kashe mayaƙan ƙungiyar da dama a harin inda ta kuma ce babu wani sojinta da ya mutu ko ya jikkata yayin artabun.

  2. Iran ta zargi Faransa da tsoma baki da kutse cikin harkokinta

    Ma'aikatar Leken Asirin Iran ta zargi gwamnatin Faransa da tsoma baki cikin harkokin cikin gida na ƙasar tare da yi mata kutse.

    A cikin wata sanarwa, ma'aikatar ta ce yayin gudanar da bincike kan wani zargin kutse daga ƙasashen waje, jami'ai sun gano wasu jami'an diflomasiyyar Faransa guda biyu a wani wurin taro na sirri da ake bincike a kai.

    Ta kuma zargi Faransa da ƙoƙarin kauce wa zarge-zargen ta hanyar yaɗa bayanai a kafafen watsa labarai.

    Iran ta ce bayan an gano jami'an diflomasiyyar, an mika su ga jakadan Faransa a Tehran ta hanyar da ta dace da dokokin diflomasiyya, tare da yin gargadin cewa za ta ɗauki mataki idan irin wannan shiga cikin harkokinta ya ci gaba.

    Sai dai tun a watan Yuli, ministan harkokin wajen Faransa Jean-Noël Barrot ya zargi jami'an tsaron Iran da keta kariyar diflomasiyya bayan da aka tsare wasu ma'aikatan ofishin jakadancin Faransa na sa'o'i da dama domin yi musu tambayoyi.

  3. Masu zaɓe sun fara kaɗa ƙuri'a a zaɓen gwamnan Osun

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Masu zaɓe a jihar Osun sun fara kaɗa ƙuri'a a zaɓen gwamnan jihar da ke gudana a ranar Asabar domin zaɓar wanda zai jagoranci jihar na shekaru masu zuwa.

    Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Najeriya (INEC) ta fara tantance masu zaɓe da kuma kaɗa ƙuri'a da misalin ƙarfe 8:30 na safe, bayan kammala rarraba kayayyakin zaɓe zuwa rumfunan zaɓe a ƙananan hukumomi 30 na jihar.

    Jihar Osun na da waɗanda suka yi rijistar zaɓe kusan miliyan 2.3, kuma ana sa ran miliyan 1.9 daga cikinsu za su kaɗa ƙuri'a a zaɓen da ke gudana tsakanin 'yan takara 15.

    Gwamna Ademola Adeleke na cikin waɗanda suka kaɗa ƙuri'arsu da sassafe, yayin da ake ci gaba da gudanar da zaɓen a sassa daban-daban na jihar.

  4. 'Maganar Trump cewa mashigar Hormuz ta Amurka ce shaci-faɗi ce'

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Jaridar Wall Street Journal ta ruwaito cewa wani jami'in Fadar White House ya ce kalaman Donald Trump na cewa mashigar Hormuz ta Amurka ce shaci-faɗi ce, ba wata manufa ta hukuma ba.

    Trump ya bayyana a ranar Juma'a cewa mashigar Hormuz mallakin Amurka ce.

    Sai dai kalaman nasa sun jawo martani daga Iran, inda mataimakin ministan harkokin wajen ƙasar, Kazem Gharibabadi, ya ce mashigar Hormuz "ta Iran ce, kuma zai ci gaba da kasancewa hakan.

  5. Mutum bakwai sun mutu a harin Isra'ila a kudancin Lebanon

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Mutum bakwai sun mutu yayin da wasu uku suka jikkata sakamakon wani hari da Isra'ila ta kai a kudancin Lebanon a safiyar Asabar, a cewar Kamfanin Dillancin Labaran Ƙasar.

    Rahotanni sun ce wani jirgin yaƙin Isra'ila ya kai hari wani gida da ke wajen ƙauyen Ansar, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutanen tare da rusa gidan gaba ɗaya.

    An kuma ruwaito cewa sojojin Isra'ila sun tarwatsa wasu gidaje a garin Bint Jbeil da ke kusa da kan iyaka.

    Wannan shi ne mafi yawan mutanen da suka mutu a hari guda tun bayan yarjejeniyar watan Yuni da ta rage faɗace-faɗace tsakanin Isra'ila da Hezbollah.

    A gefe guda, babban sakataren Hezbollah, Naim Qassem, ya zargi jami'an Lebanon da matsa wa rundunar sojin ƙasar lamba ta hanyar aiwatar da yarjejeniyar da ta haɗa da kwance ɗamarar Hezbollah da tura sojojin Lebanon zuwa kudancin ƙasar.

  6. An kai hari kan wani jirgin dakon kaya a mashigar Hormuz

    Hukumar Kula da Harkokin Kasuwancin Ruwa ta Birtaniya (UKMTO) ta ce an kai wani hari da ba a san wanda ya kai shi ba kan wani jirgin dakon kaya a mashigar Hormuz, wanda ya yi sanadin lalacewa a jikin jirgin.

    A cewar rahoton, dukkan ma’aikatan jirgin na cikin ƙoshin lafiya, kuma babu wanda ya jikkata.

    Har yanzu ba a bayyana girman ɓarnar da harin ya yi wa jirgin ba, yayin da kuma ba a san irin tasirin da lamarin zai yi ga muhalli ba..

  7. Harin Iran ya illata tsarin sufurin babban jirgin ruwan yaƙin Amurka

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Harin makamai masu linzami da jirage marasa matuƙi da Iran ta kai sansanin sojojin ruwan Amurka da ke Bahrain ya illata tsarin samar da kayayyaki ga jirgin ruwan yaƙi na USS Abraham Lincoln da sauran jiragen Amurka a yankin, in ji New York Times.

    Jaridar ta ce harin ya lalata wani muhimmin wuri na samar da kayan aiki da rundunar sojojin ruwan Amurka ke amfani da shi, lamarin da ya tilasta Pentagon ƙara dogaro da sansanin Diego Garcia mai nisa domin tallafa wa ayyukan jiragen ruwanta.

    Rahoton ya ƙara da cewa hakan ya haifar da ƙarancin wasu kayayyaki da kuma ƙarin nauyi kan ma'aikatan jiragen ruwan da ke aiki a yankin.

    USS Abraham Lincoln ya shafe kusan watanni tara yana wannan aiki, kuma ana sa ran USS George Washington zai maye gurbinsa nan gaba.

  8. Iran ta ce har yanzu ba ta yanke shawarar komawa tattaunawa da Amurka ba

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi ya ce har yanzu ƙasarsa ba ta yanke wata shawara kan komawa tattaunawa da Amurka ba, yana mai jaddada cewa tattaunawar da ya yi da Qatar da Pakistan “ba ta nufin an fara shawarwari.”

    A lokaci guda kuma, shugaban Amurka Donald Trump ya yi iƙirarin cewa bayan abin da ya kira “shan kashin da Iran ta yi”, zai ayyana mashigar Hormuz a matsayin mallakin Amurka, sai dai Tehran ta musanta batun.

    Jaridar Wall Street Journal ta ruwaito wani jami’in Fadar White House na cewa kalaman Trump wasa ne kawai.

    Trump ya kuma yi magana kan abin da ya kira “mummunar barazanar tattalin arziƙin Iran, yayin da shugaban ƙasar Masoud Pezeshkian ya yi gargaɗin raguwar kuɗaɗen shiga daga man fetur da kuma sabon hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar.

  9. Assalamu alaikum

    Masu bibiyar shafin labaran kai tsaye na BBC Hausa,barkanmu da wannan safiya ta ranar Asabar..

    Kamar kodayaushe, za mu kawo maku labarn abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Aisha Babangida ce ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokacin.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.