Arsenal na gab da ɗaukar Merino, Newcastle na son Madueke

Crystal Palace na shirin yin watsi da tayi na hudu da Newcastle ta yi na fam miliyan 65 kan ɗanwasan baya na Ingila mai shekara 24 Marc Guehi. (Sky Sports)
Ɗanwasan baya na Chelsea Trevoh Chalobah mai shekara 25 na cikin zaɓin da Newcastle United ke dibawa. (Talksport)
Palace ta amince da yarjejeniya kan ɗanwasan baya na Faransa Maxence Lacroix, mai shekara 24, tsakaninta Wolfsburg. (Sky Germany - in German)
Newcastle na iya ɗauko ɗanwasan gaba na Chelsea Noni Madueke kan fam miliyan 30 amma ta fi son ya zo a matsayin ɗanwasan aro (Football Insider)
Chelsea za ta sabunta tattaunawarta da Atletico Madrid a ƙarshen mako kan ɗanwasan tsakiya na Ingila Conor Gallagher da ɗanwasan gaba na Portugal Joao Felix, dukkaninsu ƴan shekara 24. (Telegraph - subscription required)
Tattaunawa tsakanin Arsenal da Real Sociedad kan ɗanwasan Spain na tsakiya Mikel Merino ta kai mataki na ƙarshe (Fabrizio Romano)
Merino na shirin barin tawagar Real Sociedad a wasan farko da suke shirin fafatawa da Rayo Vallecano a La Liga a ranar Lahadi. (Marca - in Spanish)
Fiorentina na son ɗauko ɗanwasan Manchester United da Sweden mai shekara 30 Victor Lindelof. (Gianluca Di Marzio - in Italian)
An faɗa wa ɗanwasan tsakiya na Tunisia Hannibal Mejbri cewa zai iya barin Manchester United amma ba a matsayin aro ba yayin da Rangers da Celtic duka suka nuna sha'awar ɗanwasan mai shekara 21. (Football Insider)
Kocin Liverpool ya tilasta wa tagawar ƙungiyar cin abincin safe tare a filin atisaye. (Times - subscription required)
Ɗanwasan gaba na Roma Tammy Abraham, mai shekara 26, na shirin zuwa Saudiyya a ƙungiyar da ba a bayyana ba duk da West Ham na son ɗanwasan na Ingila. (La Repubblica - in Italian)
Tsohon ɗanwasan tsakiya na Liverpool Thiago Alcantara ya kammala aikinsa na wuccin gadi da kocin Barcelona Hansi Flick inda yanzu ya dawo Merseyside. (Marca - in Spanish)











