Juventus ta shiga cinikin Sancho, Napoli na zawarcin McTominay

Asalin hoton, Reuters
Juventus na tattaunawa da Manchester United a kan ɗan wasan tsakiyar Ingila mai shekara 24, Jadon Sancho (Athletic subscription required),
Napoli ta na tattaunawa da Manchester United kan sayen ɗan wasan ƙungiyar McTominay, 27. (Sky Sports)
Manchester United ta amince da kwangilar sayen ɗan wasa mai shekara 18yrs, daga Guidars FC, Sekau Kone, wanda ya shana a gasar cin kofin duniya na matasa ƴan shekara nawa?
Bournemouth ta nuna sha’awar ɗaukar mai tsaron ragar Chelsea, Kepa Arrizabalaga, mai shekara 29. (Athletic - subscription required)
Da alama Arsenal ta kusa janyewa daga zawarcin ɗan wasan tsakiyar Athletic Bilbao mai shekara 22, Nico Williams, wanda ya lashe gasar Euro 2024 tare da tawagar Sifaniya. (Independent), external
Porto ta ƙulla yarjejeniya da Arsenal domin dawo da ɗan wasan Sifaniya mai shekara 26, Fabio Vieira wanda ke zaman aro a Arsenal ɗin. A cikin watan Yulin 2022 ɗan wasan Portugal ɗin ya koma taka leda a Asernal a mastayin ɗan wasan aro. (Mail)
Tsohon ɗan wasan bayan West Ham mai shekara 36 Angelo Ogbonna, ya shirya komawa taka leda a ƙungiyar Watford dake buga gasar Championship. (Watford Observer)
Aston Villa da Bologna sun amince da yarjejeniyar aron ɗan wasan tsakiya mai shekara 20, Samuel Iling-Junior. (Fabrizio Romano)
Liverpool na bibiyar ɗan wasan bayan Bayer Leverkusen da Ecuador, Piero Hincapie. (Football Insider)














