Arteta ya jinkirta tattaunawa da Arsenal kan kwantiragi

Mikel Arteta

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Kocin Arsenal Mikel Arteta ya ce zai fara tattaunawa da ƙungiyar kan sabon kwantaraginsa da zarar an rufe kasuwar saye da sayar da ƴan wasa na bana.

Kwantiragin Arteta na yanzu zai ƙare ne a ƙarshen kakar wasa ta bana amma tattaunawar ba za ta zama matsala ba kuma kocin mai shekaru 42 yana da kyakkyawar alaƙa da shugabannin ƙungiyar.

Arteta ya ce "An mayar da hankali ne kan kasuwar musayar ƴan wasa.

"Muna da abubuwa da yawa da za mu tattaunawa a kai. Muna kan hakan kuma za mu warware komai idan lokaci ya yi."

Kocin ɗan kasar Sifaniya ya kasance kocin Arsenal tun a shekarar 2019 kuma ya jagoranci ƙungiyar zuwa matsayi na biyu a kakar wasannin Premier biyu da suka gabata.

Gunners sun taka rawar gani a kasuwar musayar ƴan wasan wannan bazarar, inda suka sayi ɗan wasan baya na Italiya Riccardo Calafiori a kan kuɗi fan miliyan 42 tare da sayar da Emile Smith Rowe ga Fulham kan farashin da zai kai fan miliyan 34.