Gundogan ya sake komawa Manchester City

Asalin hoton, Getty Images
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1
Ɗan ƙwallon Jamus, Ikay Gundogan ya koma Manchester City, inda ya saka hannu a kwantiragin shekara ɗaya.
Ɗan wasan ya dawo ƙungiyar, wadda ke riƙe da kambun Gasar Premier ɗin ya koma Barcelona kimanin wata 12 da suka gabata.
Gundogan ya kwashe shekara bakwai a Manchester City, inda ya lashe kofuna da dama, har ya kai ga zama kyaftin ɗin ƙungiyar.
Ya kwatanta lokacinsa a Manchester City a matsayin "wadataccen lokaci", sannan ya ce ya ƙagu ya cigaba taka leda a ƙungiyar.
Gundogan na cikin ƴan wasan da suka fi ɗaukar albashi a Barcelona, wanda tafiyarsa zai taimaka wa ƙungiyar wajen daidaita da kashe kuɗinsu domin gudun karya doka.






