Trippier na son barin Newcastle United a watan nan

Kieran Trippier

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Mai tsaron bayan Newcastle United, Kieran Trippier na son barin ƙungiyar a watan nan, domin ya samu inda zai ke buga wasanni yadda ya kamata.

Mai shekara 33 ɗan wasan tawagar Ingila, ya yi zaman benci a wasan makon farko a Premier League da Newcastle ta ci Southapton 1-0 a St James Park ranar Asabar.

Trippier, ya koma buga Premier League daga Atletico Madrid a 2022, amma ana amfani da Tino Livramento a gurbin tsare baya daga gefen hagu a Newcastle.

Newcastle United ta hana Tripper ya bar ƙungiyar a watan Janairu, bayan da Bayern Munich ta yi zawarcinsa da wasu ƙungiyoyin da ke buga gasar Saudi Arabia

Wasu na cewa Tripper na ƙwaɗayin komawa Everton, domin taka leda karkashin Sean Dyche, wanda ya horar da shi a lokacin da ya buga wa Burnley tamaula.

Everton za ta je Tottenham, domin buga wasan mako na biyu a Premier League a karshen makon nan, sai dai za ta kara ba tare da Ashley Young ba, wanda aka bai wa jan kati a karawa da Brighton.

Trippier, wanda ya buga wa Ingila wasa 54, ya yi mata dukkan wasa shida a Euro 2024, amma sai aka ajiye shi a benci a wasan karshe aka sa Luke Shaw.

Tsohon ɗan wasan Tottenham yana da ƙunshin yarjejeniyar kaka biyu da ta rage masa a St James Park.