Arsenal da Newcastle na gogayya kan Mohammed Kudus

Asalin hoton, Reuters
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta West Ham na da niyyar sayar da ɗan ƙwallon Ghana Mohammed Kudus idan ta samu "babban tayi" a watan Janairu, kamar yadda shafin TalkSPORT ya ruwaito.
Rahoton ya ce Arsenal na duba yiwuwar sayen ɗanwasan tsakiyar, wanda ke da farashin fam miliyan 85 a ƙunshin yarjejeniyarsa da Hammers ɗin.
Sai dai kuma, akwai yiwuwar sai Arteta ya sayar da wasu 'yanwasan kafin ya iya sayen Kudus.
A gefe guda kuma, Newcastle United na shirin fafatawa da Arsenal ɗin da ma Liverpool wajen saye Kudus, a cewar rahoton Daily Express.
Rahoton ya nuna cewa Hammers ta yi wa ɗanwasan kuɗi fam miliyan 90, yayin da Newcastle ke da niyyar gwada sa'arta a kansa.
Kudus na cikin manyan 'yanwasan West Ham duk da cewa ƙwallo biyu kawai ya ci zuwa yanzu tare da bayar da ɗaya a zira a raga a kakar wasa ta bana.







