Trippier zai koma Turkiya, Gundogan na da damar ci gaba da taka leda a City

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Ɗanwasan baya na Newcastle mai shekara 33 Kieran Trippier, wanda ya ya yi ritaya da buga wa Ingila wasa a makon da ya gabata ya amince da yarjejeniya da ƙungiyar Turkiya Eyupspor. (Sportsdigitale - in Turkish)

An yi wa ƙungiyar Fenerbahce ta Mourinho tayin ɗanwasan Chelsea da England Ben Chilwell, mai shekaru 27. (Givemesport)

Kungiyar Anderlecht ta Belgium na son ɗanwasan tsakiya na Manchester United da Denmark Christian Eriksen, mai shekara 32. (Het Belang van Limburg - in Dutch),

Ɗanwasan tsakiya na Manchester City mai shekara 33 Ilkay Gundogan yana da damar tsawaita kwangilar shi a ƙungiyar idan har ya haska sama da kashi 50 na wasannin kakar bana. (Star)

An ajiye ɗanwasan gaba na Napoli Victor Osimhen daga tawagar ƙungiyar, wanda Chelsea ke nema (La Gazzetta dello Sport - in Italian)

Liverpool na son ɗauko ɗanwasan tsakiya a Janairu bayan ta kasa samu a bazara. (Football Insider)

Ɗanwasan gaba na Ingila Raheem Sterling, mai shekara 29, ya yi watsi da tayin albashin fam 650,000 a mako daga Saudiyya inda ya gwammace ya taka leda a Arsenal a matsayin aro daga Chelsea. (Mirror)

Nottingham Forest ta yi watsi da tayin Newcastle kan danwasan gaba na Sweden Anthony Elanga, mai shekara 22. (Sky Sports)

Ɗanwasan Netherland da Arsenal Omar Rekik, mai shekara 22, ya kawo karshen yarjejeniyarsa. (Fabrizio Romano)