Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Liverpool za ta ci gaba da zawarcin Guehi, Osimhen zai ɗumama benci a Napoli
Ƙila Liverpool za ta nemi ɗaukar ɗan wasan bayan Ingila da Crystal Palace mai shekara 24, Marc Guehi a ƙarshen kakar wasan bana, lokacin da kwangilarsa za ta rage saura shekara ɗaya kacal. Newcastle ta yi zawarcin Guehi a bana. (Mirror)
Manchester United ta ƙi amincewa da tayin da Real Betis ta gabatar mata na neman ɗaukar ɗan wasan ta na gefe kuma ɗan Brazil mai shekara 24, Antony, da kuma ɗan wasan tsakiyar ta ɗan ƙasar Denmark mai shekara 32, Christian Eriksen. (Mail)
Ɗan wasan gaban Najeriya mai shekara 25, Victor Osimhen ba zai samu shiga tawagar Napoli ba, bayan tattaunawar cinikin sa ta watse tsakanin Napoli da Chelsea. (Gianluca di Marzio on X)
Chelsea ta dakatar da cinikin ɗan wasan gabanta, Deivid Washington ga Strasbourg a kan £16.8m bayan tsoron da ya taso cewa ƙungiyoyin biyu za su iya karya doka a kan cinikin saboda dukkan su kamfanin BlueCo ne ya mallake su. (L’Equipe - in French)