Eguavoen ya maye gurbin Labbadia a kociyan Super Eagles

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Hukumar ƙwallon kafa ta Najeriya ta ce Augustine Eguavoen ne zai ja ragamar Super Eagles maimakon Bruno Labbadia.

A makon jiya ne Nff ta sanar da naɗa Labbadia ɗan kasar Jamus a matakin sabon kociyan tawagar Najeriya, domin maye gurbin Finidi George.

To sai dai Nff ta wallafa a shafinta na intanet cewar wasu tsauraran dokoki na hukumomin harajin Jamus ya sa a soke yarjejeniyar da aka kulla tsakaninta da koci, Labbadia.

“Kwanaki uku da suka gabata mun tattauna kan batun haraji, kuma na fada musa karara cewa babu yadda za a yi NFF ta amince a biya masa kaso na karin harajin da Jamus za ta nema. Ba zai yiwu mu sauke nauyin da ya rataya a wuyan mu na fitar da wani kudi tsakanin kashi 32% zuwa 40% na albashinsa ba, bayan biyan albashin da aka amince da shi a duk wata.

“NFF da Mista Labbadia mun cimma yarjejeniya kafin mu bayyana cewa zai zama kocin Super Eagles. Babu batun haraji a lokacin da muka tattauna da shi, kuma shi da kansa ya amince da duk sharuɗɗan kafin batun haraji ya fito. Mun yi iya bakin kokarinmu don mu sasanta amma ya jajirce cewa hukumar NFF ma ta biya cikakken adadin haraji. Ba za mu iya yin hakan ba, "in ji shugaban NFF, Ibrahim Musa Gusau.

Saboda haka daraktan tsare-tsare na hukumar ƙwallon kafar Najeriya, Augustine Eguavoen shi ne zai ja ragamar wasan neman shiga gasar cin kofin Afirka da Super Eagles za ta buga cikin watan Satumba.

Najeriya za ta karɓi bakuncin Benin ranar 7 ga watan Satumba, sannan kwana uku tsakani ta fafata da Rwanda a Kigali.

Morocco ce za ta karbi bakuncin gasar cin kofin Afirka a 2025.

Wannan shi ne karo na huɗu da Eguavoen zai horar da Super Eagles, bayan 2005-2007 da 2010 da kuma 2022.