Toney na Brentford ya koma Al-Ahli ta Saudi Arabia.

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Ɗan wasan Brentford, Ivan Toney ya saka hannu kan yarjejeniyar taka leda a gasar tamaula ta Saudi Arabia a ƙungiyar Al-Ahli.

Tun a ranar Juma'a mai buga Premier League ta amince da farashin £40m ƙudin ɗan wasan mai shekara 28, inda aka tabbatar da cinikin da safiyar Asabar.

Toney yana cikin ƴan wasan da Gareth Southgate ya je da su Euro 2024 a Jamus, wanda ya shiga wasa uku a canjin ɗan ƙwallo - har da wanda Sifaniya ta lashe kofin.

Ya ci bugun fenariti a lokacin da Ingila ta yi waje da Switzerland.

Toney ya ci ƙwallo 20 a gasar Premier League a 2022/23 da zura biyar a bara, bayan da ya kammala hukuncin dakatarwa bisa ƙarya dokar yin caca ta hukumar ƙwallon kafar Ingila.

Sai dai kociyan riƙon ƙwarya, Lee Carsley bai gayyaci Toney ba cikin waɗan da za su buga wa Ingila Nations League a watan Satumba - wanda ya yi wasa shida da cin ƙwallo ɗaya.