City ta ƙayyade farashin McAtee, Man Utd za ta ƙaro sabbin ƴanwasa

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Manchester City ta ƙayyade farashi fam miliyan 35 kan ɗanwasan tsakiya na Ingila James McAtee, mai shekara 22, wanda West Ham da Eintracht Frankfurt rubibinsa. (Telegraph - subscription)

Real Madrid za ta jira har baɗi kafin ɗauko ɗanwasan baya na Liverpool da Faransa Ibrahima Konate, mai shekara. (Football Insider)

An ɗage sabunta kwangilar ɗanwasan gaba na Brazil da Real Madrid Vinicius Jr, mai shekara 25, har sai zuwa 2026. (AS - in Spanish)

Real Madrid na sa ido kan ɗanwasan Arsenal da Faransa William Saliba, mai shekara 24. (L'Equipe - in French)

Leeds United na son hamayya kan ɗanwasan Spain na gaba Mateo Joseph, mai shekara 21 da nufin samun kuɗin karɓo ɗanwasan gaba na Brazil da Fulham Rodrigo Muniz, mai shekara 24. (Sun)

Kocin Manchester United Ruben Amorim na son sake shiga kasuwa domin ƙaro wasu sabbin ƴanwasa. (Mirror)

Haka kuma United ta taya ɗanwasan gaba na Sporting Viktor Gyokeres, mai shekara 27, tare fatan janyo ra'ayin ɗanwasan zuwa Old Trafford maimakon Arsenal. (A Bola - in Portuguese)

Kuma tana son ɗanwasan gaba na Italiya Francesco Pio Esposito, mai shekara 20, tayin da Inter Milan ta yi watsi a Janairu. (Football Italia - in Italian)

Manchester United ta kamma diba lafiyar ɗanwasan gaba na Kamaru Bryan Mbeumo, mai shekara 25, wanda ta karɓo daga Brentford. (Fabrizio Romano)

Nottingham Forest na kan gaba wajen buƙatar ɗanwasan tsakiya na Ingila Jacob Ramsey, mai shekara 24, daga Aston Villa. (Football Insider)