Juve za ta biya kuɗin Sancho, Chelsea za ta yi gwanjon Sterling

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Juventus na dab da kammala cinikin ɗanwasan Ingila Jadon Sancho daga Manchester United yayin da ƙungiyoyin biyu suka cimma matsaya kan farashin ɗanwasan na gaba mai shekara 25. (Tuttosport - in Italian)

Juventus a shirye take ta biya farashin da Manchester United take nema sama da fam miliyan 21 kan Sancho wanda ya ƙulla yarjejeniyar shekara huɗu da Juve. Sportmediaset - in Italian)

Liverpool ce kan gaba wajen buƙatar ɗanwasan tsakiya na Crystal Palace da Ingila Adam Wharton, mai shekara 21, inda ta sha gaban Tottenham - amma ɗanwasan na son ya ƙara yin shekara gudana a Selhurst Park. (Sun on Sunday)

Manchester United da Newcastle United na hamayya kan ɗanwasan gaba na Paris St-Germain da Faransa Randal Kolo Muani, mai shekara 26. (Footmercato - in French)

Golan Everton da Ingila Jordan Pickford, mai shekara 31, na dab da sanya hannu kan sabuwar kwangilar shekara huɗu a ƙungiyar ta Merseyside. (Sun on Sunday)

Bayern Munich na samun ci gaba kan buƙatar karɓo ɗanwasan gaba na Liverpool Luis Diaz bayan watsi da tayinta har sau biyu. Ana sa ran ƙungiyoyin biyu za su tattauna kan ɗanwasan mai shekara 28 na Colombia. (Bild - in German)

Fenerbahce ta cimma yarjejeniyar ɗauko ɗanwasan baya na Slovakia Milan Skriniar, mai shekara 30, da ɗanwasan tsakiya na Spain Marco Asensio, mai shekara 29 daga Paris St-Germain. (Footmercato - in French)

Ɗanwasan gaba na Gabon striker Pierre-Emerick Aubameyang, mai shekara 36, ya yi watsi da buƙatarsa da Al-Ettifaq ta yi bayan ya baro Al-Qadsiah amma ɗanwasan ya zaɓi ya koma Marseille. (Footmercato - in French)

Chelsea na fatan sayar da ɗanwasan gaba na Ingila Raheem Sterling kan fam miliyan 20m, domin dawo da wani kaso na kuɗin da ta biya Manchester City fam miliyan 47.5 shekaru uku da suka gabata. (Sun on Sunday)

Tottenham na tattaunawa da Bayern Munich domin sayen ɗanwsan tsakiya na Portugal Joao Palhinha, amma dole sai ta biya fam miliyan 26 kan ɗanwasan mai shekara 30 . (Christian Falk)