Arsenal na ci gaba da matsa ƙaimi a yunƙurinta na sayen
dan wasan gaba Viktor Gyokeres daga kungiyar Sporting CP domin cike gibin da
take da shi na rashin tsayayyen mai ɗaga raga.
Sai dai lamarin na ta jan ƙafa inda har magoya bayan ƙungiyar ke nuna gajiyawa kan abin da suke gudu ya zama ‘jiran gawon shanu’.
Sai dai ana ganin cewa yanzu akwai haske kan yunkurin,
inda ake ganin cewa yana gab da tafiya Emirates.
Tun a makon jiya ne BBC ta ruwaito cewa an kai matakin ƙarshe a cinikin ɗan wasan kan kuɗi fam miliyan 63.5, sai dai daga baya an tsaya ana tataɓurza tsakanin Arsenal da Sporting kan sauran kuɗaɗen tsarabe-tsarabe.
Gyokeres dai ya riga ya amince cewa zai tafi Arsenal kan kwantaragi mai tsawon shekara biyar.
An shafe shekaru ana kiraye-kirayen cewa ya kamata Arsenal
ta dauko garnannen mai zura zura kwallo, abin da ake ganin tamkar Arteta ya yi
kunnen uwar-shegu da su.
Gyokeres dan asalain kasar Sweden ya zura kwallo 39 a
kakar da ta gabata – fiye da kowane dan wasa a manyan gasannin kungiyoyin Turai
guda takwas.
Idan sayen Gyokeres ya tabbata, zai zama daya daga cikin
cinikin dan wasa da ya fi jan hankali a wannan lokaci na musayar ‘yan wasa.
Ganin cewa ɗan wasan gaba na Arsenal Gabriel Jesus zai kai
ƙarshen wannan shekara yana jinya, ana kallon Viktor a matsayin wanda
ya dace da Arsenal a wannan lokaci ganin cewa ba a cika yi wa Kai Haverts kallon
cikakken lamba 9 ba.
Gyokeres ya ƙware wajen riƙe ƙwallo da gudu da ita a ƙafarsa
da kuma kutsawa ta tsakiyar masu tsaron baya.
Haka nan ɗan ƙwallon na da ɗan karen gudu, wanda ake ganin
wannan ma zai taimaka wa Arsenal.