Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man Utd na son Osimhen, Arsenal ta nace wa Raphinha
Chelsea ta fara tunanin ɗauko golan Liverpool da Jamhuriyyar Ireland Caoimhin Kelleher, mai shekara 25. (Sun)
Manchester United na son ɗanwasan gaba na AC Milan da Amurka Christian Pulisic, mai shekara 26, kamar yadda Liverpool da West Ham ke rabibin ɗanwasan. (Calciomercato)
Ruben Amorim zai yi aiki da madaidacin kasafin kuɗi kamar Erik ten Hag kuma ƙalubalen da ke gabansa shi ne farfaɗo da tawagar. (Telegraph - subscription required)
Amma Manchester United na diba yiyuwar yin musaya inda ɗanwasan gaba na Netherlands Joshua Zirkzee, mai shekara 23, ya koma Napoli, yayin da ɗanwasan gaba na Najeriya Victor Osimhen, mai shekara 25, ya koma Old Trafford. (Calcio Napoli)
Ana sa ran ɗanwasan tsakiya na Manchester United da Denmark Christian Eriksen, mai shekara 32, zai bar ƙungiyar a ƙarshen kaka. (Fabrizio Romano, external)
West Ham da Fulham na hamayya kan ɗanwasan Manchester City da Ingila mai shekara 21 James McAtee. (Guardian)
Arsenal na son ɗanwasan Brazil Raphinha kuma rahotanni sun ce a shirye take ta biya fam miliyan 75. Sai dai Barcelona ba ta son rabuwa da ɗanwasan. (Fichajes - in Spanish)
Nottingham Forest za ta yi watsi da duk tayi kan ɗanwasan Brazil na baya Murillo, mai shekara 22, a watan Janairu yayin da Real Madrid ke cikin ƙungiyoyin da ke son ɗanwasan. (Football Insider)
Liverpool da Arsenal ba za su iya ɗauko ɗanwasan gaba na Ghana ba Mohammed Kudus kan farashinsa da ya kai ƙasa da fam miliyan 85, yayin da West Ham za ta ci gaba da gwada sa'arta. (Football Insider)
Chelsea, Manchester City da Tottenham na hamayya kan ɗanwasan baya na Bournemouth da Ukraine Illia Zabarnyi. (Teamtalk)
Tottenham na son ɗauko ɗanwasan tsakiya na Valencia da Spain Javi Guerra, mai shekara 21. (GiveMeSport)
Ɗanwasan tsakiya na Faransa Paul Pogba, mai shekara 31, na son ci gaba da taka leda a manyan ƙungiyoyin Turai bayan ya raba gari da Juventus. (ESPN)
Ɗanwasan baya na Bayer Leverkusen da Jamus Jonathan Tah, mai shekara 28, zai fara tattaunawa da ƙungiyoyin da ke buƙatarsa a Janairu yayin da yake son barin ƙungiyar ta Bundesliga idan kwangilar shi ta kawo ƙarshe. Barcelona, Real Madrid da Bayern Munich na cikin ƙungiyoyin da ke ribibin ɗanwasan. (Mundo Deportivo)
Tsohon ɗanwasan Brazil Ronaldo na shirin ƙaddamar da yakin neman zaɓe domin zama shugaban ƙwallon Brazil a 2026 kuma yana son ɗauko kocin Manchester City Pep Guardiola a matsayin mai horar da ƴanwasan ƙasar. (L'Equipe - in French)