Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man Utd na farautar Danilo, Madrid na son dawo da Ramos
Ruben Amorim na son ɗauko ɗanwasan baya na Juventus Danilo, mai shekara 33, a matsayin ɗanwasan farko da zai ɗauko a Manchester United a Janairu, yayin da kwangilar ɗanwasan na Brazil ke dab da ƙarewa. (Mirror)
Arsenal ta tuntuɓi ɗanwasan baya na Sporting Ousmane Diomande, mai shekara 20, kodayake Chelsea da Bayern Munich na son ɗanwasan na Ivory Coast. (Metro)
Real Madrid na nazarin dawo da Sergio Ramos, mai shekara 38 daga Sevilla domin maye gurbin ɗanwasan baya na Brazil Eder Militao, mai shekara 26. (Fichajes - in Spanish)
Barcelona ta dakatar da bukatar karɓo ɗanwasan Liverpool da Ingila Trent Alexander-Arnold, mai shekara 26 domin sacewa da matashin ɗanwasan ƙungiyar Lamine Yamal, mai shekara 17. (Football365)
Kocin Barca Hansi Flick na son ɗauko ɗanwasan baya Alphonso Davies, mai shekara 24, idan har ɗanwasan ya yanke shawarar watsi da tayin Bayern Munich - kodayake Real Madrid da Manchester United na ribibin ɗanwasan. (Christian Falk, Bild)
Liverpool na shirin taya ɗanwasan gaba na Masar da Eintracht Frankfurt Omar Marmoush, 25 kan sama da fam miliyan 58. (Fichajes - in Spanish)
Liverpool na dab da cimma yarjejeniya da Real Madrid kan ɗanwasan tsakiya na Faransa Aurelien Tchouameni, mai shekara 24. (Teamtalk)
Manchester City na fatan ƙarfafa tsakiyarta inda take farautar ɗanwasan tsakiya na Real Sociedad Martin Zubimendi, mai shekara 25, yayin da Liverpool ita ma ke farautar ɗanwasan na Spain. (Football Insider)
Sabon Kocin Manchester United Amorim ba zai ɗauko ƴanwasa daga Sporting ba a wannan Janairu wanda hakan zai ba Manchester City da Arsenal da Paris St-Germain damar ɗauko ɗanwasan gaba na Sweden Viktor Gyokeres, mai shekara 26. (Mirror)
Amma Amorim na son ɗanwasan tsakiya na Norway mai shekara 17 Sverre Nypan daga Rosenborg. (GiveMeSport)
Tsohon Kocin Manchester City da Italiya Roberto Mancini na kan gaba domin maye gurbin kocin Roma ɗan ƙasar Croatia Ivan Juric, yayin da shugabannin ƙungiyar aka sa ran za su tantance makomarsa bayan wasan Bologna. (La Gazzetta dello Sport - in Italian)
Tottenham da West Ham da Chelsea na sa ido kan ɗanwasan baya na Gent Archie Brown, mai shekara 20, amma sai a 2027 kwangilar ɗanwasan za ta kawo ƙarshe. (TBR Football)
Ɗanwasan baya na Dinamo Tbilisi mai shekara 16 na jan hankalin Real Madrid da Barcelona. (AS - in Spanish)