Likitoci sun nuna damuwa game da lafiyar Sarauniyar Ingila

Asalin hoton, Getty Images
Fadar Buckingham ta bayyana cewa likitoci na sa ido a kan lafiyar Sarauniyar Ingila bayan da suka nuna damuwa game da koshin lafiyarta.
Wata sanarwar daga fadar ta ce "Likitocin sarauniyar sun damu kan halin lafiyarta bayan da suka duba ta da safiyar ranar Alhamis, sun kuma ba da shawarra cewa likitoci za su ci gaba da kula da ita."
"Sarauniya tana samun sauƙi a Balmoral. Yarima Charles da jikanta Yarima William a yanzu suna tare da ita.
"Kazalika surukarta Duchess of Cornwall ita ma ta tafi Balomral ɗin."
Sanarwar na zuwa ne bayan da aka janye sarauniyar mai shekara 96 daga wani taron majalisarta na intanet da ake yi a ranar Laraba, inda likitoci suka bayar da shawarar cewa tana buƙatar hutu.
Firaminista Liz Truss ta ce “dukkan al’ummar Ingila na cikin damuwa” da jin labarin.
Addu’ata da ta dukkan al’ummar Birtaniya na tare da Ranta ya daɗe Sarauniya tare da iyalanta a wannan lokaci,” ta ƙara da cewa.
A ranar Talata ne Sarauniya ta tabbatar da Liz Truss a matsayin sabuwar Firaministar Birtaniya a fadar Balmoral, maimakon ta tafi Landan don yin hakan.
A tsawon shekara 70 da ta shafe tana mulki, sarauniya kan gana ne da kowane sabo ko sabuwar firaminista a Fadar Buckingham.
Tana yin hutun lokacin bazara ne a gidanta da ke Scotland tun watan Yuli.















