Sarauniya Izabel ta Ingila ta cika shekara 70 a kan karagar mulki, kuma hakan ya sa ta zamo ta farko da ta yi wannan daɗewar a cikin jerin sarakunan da suka yi mulki a ƙasar.
Domin bikin wannan rana ce muka zaɓo wasu hotuna a ma'ajaiyar PA Media na rayuwarta tun daga haihuwa.
1926
Asalin hoton, PA Media
Bayanan hoto, An haifi sarauniya ranar 21 ga watan Afrilun 1926 a London, kuma ita ce ƴa ta farko ga Albert, Duke na York, da matarsa da aka fi sani da Lady Elizabeth Bowes-Lyon.
1927
Asalin hoton, PA Media
Bayanan hoto, An gabatar da jaririya Elizabeth ga al'ummar ƙasar, wadda ake sa ran za ta zama sarauniya wata rana. A tare da ita iyayenta ne da kuma Sarki George V da kuma Queen Mary.
1947
Asalin hoton, PA Media
Bayanan hoto, A ranar 20 ga watan Nuwamban 1947 ne aka ɗaura aurenta da wani ɗan uwanta na nesa Yarima Philip na Girka, a Westminster Abbey.
1948
Asalin hoton, PA Media
Bayanan hoto, A shekarar 1948 ne ta haifi danta na fari Charles.
1950
Asalin hoton, PA Media
Bayanan hoto, A shekarar 1950 aka yi wa Charles ƙanwa mai suna Anne.
1952
Asalin hoton, PA Media
Bayanan hoto, A watan Fabrairun 1952 ne mahaifinta ya rasu a lokacin ta je Kenya wata ziyara ita da mijinta.
1953
Asalin hoton, PA Media
Bayanan hoto, A watan Yunin 1953 aka naɗa ta sarautar Birtaniya. inda miliyoyin mutane suka kalli bikin naɗin a talabijin.
1960
Asalin hoton, PA Media
Bayanan hoto, Yarima Andrew ne ɗan da ta fara haifa bayan hawanta mulki kuma shi ne ɗan da aka haifa a karagar sarauta cikin shekara 103.
1963
Asalin hoton, PA Media
Bayanan hoto, A nan Sarauniya ce ke komawa Fadar Buckingham bayan halartar wani biki na sukuwar sarakai. Duk shekara tana halartar bikin tuna ranar haihuwarta inda ake yin fareti, sai a shekarar 1955 ne kawai ba ta yi ba saboda wani yajin aiki, sai kuma a shekarar 2020 ma annobar cutar korona ta hana yin bikin.
1964
Asalin hoton, PA Media
Bayanan hoto, Sarauniya ta ci gaba da ƙoƙarin kyautata alaƙa a gida da ƙasashen waje.
1967
Asalin hoton, PA Media
Bayanan hoto, Sarauniya a wajen wata liyafa a Asibitin Masarauta da ke Chelsea, don yin bikin hsekara 50 da shigar mata al'amuran ayyukan gwamnati.
1968
Asalin hoton, PA Media
Bayanan hoto, Sarauniya da mijinta da ƴaƴanta sun cakare a wannan hoton.
1969
Asalin hoton, PA Media
Bayanan hoto, Sarauniya Elizabeth II ta naɗa ɗantaYarima Charles a matsayin Yariman Wales a yayin wani biki a Fadar Caernarfon. Tun yana shekara tara aka ambaci nadin nasa amma sai da ya ƙara girma sannan aka yi masa naɗin.
1972
Asalin hoton, PA Media
Bayanan hoto, Sarauniya kenan a wani ɗakin karatu a Balmoral a shekarar da ta cika 25 da aurenta. Ba ta Landan a lokacin.
1974
Asalin hoton, PA
Bayanan hoto, Elizabeth celebrates ta yi bikin cikarta shekara 48 a Fadar Windsor Castle.
1976
Asalin hoton, PA Media
Bayanan hoto, Nan kuma a lokacin da ta cika shekara 50 ne da haihuwa suka yi hoto ita da mijinta da karamin ɗanta Yarima Edward mai shekara 12 a Fadar Windsor.
1977
Asalin hoton, PA Media
Bayanan hoto, Sarauniya ta yi bikin cika shekara 25 a karagar mulki inda ta yi wani rangadi a Birtaniya - ta kuma ziyarci gundumomi 36 Tcikin mako 10.
1979
Asalin hoton, PA
Bayanan hoto, A shekarar 1979 ta ziyarci ƙasar Oman, kuma an gan ta tana zagaye a birnin Muscat.
1983
Asalin hoton, PA Media
Bayanan hoto, Sarauniya Elizabeth tana amsa gaisuwar ban girma da aka shirya mata a babban filin jirgin sama na Jomo Kenyatta a Kenya. Sarauniyar ta ziyarci dukkan ƙasashen rainon Ingila 53 ban da Kamaru da Rwanda.
1984
Asalin hoton, PA Media
Bayanan hoto, Ga sarauniya da mahaifiyarta da Yarima Charles da jikokinta biyu a lokacin raɗin sunan Yarima Harry. Sarauniya na da jikoki takwas da tattaɓa-kunni 12.
1997
Asalin hoton, PA Media
Bayanan hoto, A wannan shekara ce masarautar Ingila ta shiga ruɗanin mutuwar Gimbiya Diana.
2000
Asalin hoton, PA Media
Bayanan hoto, Sarauniya Elizabeth II da mahaifiyarta a keken dawaki a rukunin gidaje na Sandringham da ke Norfolk. Sarauniuya ta shaku da mahaifiyarta kuma suna da ra'ayoyi iri ɗaya.
2006
Asalin hoton, PA Media
Bayanan hoto, Tana duba wasu katunan taya murna da aka aike mata a lokacin da ta cika shekara 80 a duniya.
2012
Asalin hoton, PA Media
Bayanan hoto, Nan kuma a wajen bikin cikarta shekara 60 ne da hawa karagar mulki.
2015
Asalin hoton, PA Media
Bayanan hoto, A wannan shekara ta 2015 da misalin ƙarfe 5.30 na yammacin ranar 9 ga Satumba Sarauniya Elizabeth ta cika kwana 23,226 da awa 16 da minti 30 a mulki days - inda ta wuce kakarta Sarauniya Victoria.
2016
Asalin hoton, PA Media
Bayanan hoto, Sarauniya ta cika shekara 90 a duniya.
2021
Asalin hoton, PA Media
Bayanan hoto, Sarauniya na zaune ita kaɗai a wajen jana'izar mijinta Yarima Philip don nuna misali ga mutane na kiyaye dokokin annobar cutar na hana cakuduwar a wajen jana'izar. t
2022
Asalin hoton, PA Media
Bayanan hoto, Tana duba kundin da ka tsara na tunawa da rayuwarta a lokacin bikin cikarta shekara 70 a mulki.