Sarauniyar Ingila ta kamu da korona

The Queen

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Daga Dulcie Lee
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • An wallafa

Sarauniya Elizabeth ta Ingila ta kamu da cutar korona, kamar yadda fadar Buckingham ta sanar.

Fadar ta bayyana cewa sarauniya na tattare da alamun sanyi amma ana sa ran za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta sama-sama a Windsor a mako mai zuwa.

"Za a ci gaba da duba lafiyarta kuma za a bi duka hanyoyin da suka dace," kamar yadda fadar ta bayyana a wata sanarwa da ta fitar.

Sarauniya Elizabeth mai shekara 95 ta haɗu da babban ɗanta kuma magajinta wato Yarima Charles wanda shi ma ya kamu da korona a makon da ya gabata.

Sanarwar na zuwa ne mako guda bayan da sarauniyar ta kafa tarihi ta zama wadda ta fi daɗewa kan karagar mulki a tarihin Masarautar Ingila bayan ta cika shekara 70 a kan mulki a ranar 6 ga watan Fabrairu.

Wakilin BBC a Masarautar Ingila Nicholas Witchell ya bayyana cewa babu shakka sarauniya an yi mata riga-kafin korona zagaye na farko da na biyu.

Ya bayyana cewa tana bin rayuwa a hankali a ƴan kwanakin nan tun da ta kwana a asibiti a Oktobar bara yayin da ta je duba lafiyarta.