Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Shin ko Man City na turbar maimaita bajintar da ta yi a bara?
Manchester City ta kai zagayen daf da karshe a FA Cup, za ta fafata da Chelsea a Wembledon a zagayen gaba cikin watan Afirilu.
City ta kawo wannan matakin ne, bayan da ta ci Newcastle United 2-0 ranar Asabar, kuma Bernardo Silva ne ya ci mata kwallayen a zagayen daf da na kusa da na karshe.
City wadda ke fatan buga wasan karshe a FA Cup karo na 13, wadda ta lashe na bara tana da shi bakawi jimilla.
Kenan kungiyar Etihad za ta buga daf da karshe a FA Cup da Chelsea a watan gobe, sannan za ta kara da Real Madrid zagayen kwata fainals a Champions League.
Haka kuma kungiyar da Pep Guardiola ke jan ragama tana ta uku a teburin Premier League da tazarar maki daya tsakaninta da Liverpool ta biyu da kuma Arsenal mai jan ragama da maki 64.
A kakar da ta gabata ta 2022/23, City ta dauki kofi uku da ya hada da FA Cup, bayan da ta doke Manchester United 2-1 ranar 3 ga watan Yunin 2023.
Haka kuma kungiyar ce ta lashe Premier League na bara kuma na uku jimilla, wadda ta kammala da maki 89, sai Arsenal ta biyu mai maki 84.
Daga nan ne City ta lashe Champions League a karon farko a tarihi, bayan da ta yi nasara a kan Inter Milan da cin 1-0 ranar 10 ga watan Yuni.
Wasannin da ke gaban Manchester City kafin kammala kakar bana
Premier League Lahadi 31Maris din 2024
- Man City da Arsenal
Premier League Laraba 3 ga watan Afirilun 2024
- Man City da Aston Villa
Premier League Asabar 6 ga watan Afirilun 2024
- Crystal Palace da Man City
Champions League Talata 9ga watan Afirilun 2024
- Real Madrid da Man City
Premier League Asabar 13 ga watan Afirilun 2024
- Man City da Luton
Champions League Laraba 17 ga watan Afirilun 2024
- Man City da Real Madrid
Premier League Asabar 20 ga watan Afirilun 2024
- Tottenham da Man City
English FA CUP Asabar 20 ga watan Afirilun 2024
- Man City da Chelsea
Premier League Asabar 27ga watan Afirilun 2024
- Nottm Forest da Man City
Premier League Asabar 4 ga watan Mayun 2024
- Man City da Wolves
Premier League Asabar 11 ga watan Mayun 2024
- Fulham da Man City
Premier League Lahadi 19 ga watan Mayun 2024
- Man City da West Ham