Real Madrid ta kusan lashe La Liga na bana na 36 jimilla

An wallafa

Real Madrid na daf da lashe kofin La Liga na bana na 36 jimilla, bayan da take ta daya a kan teburi da maki 72, saura wasa tara a kammala kakar bana.

Ranar Asabar Real ta je ta doke Osasuna da cin 4-2 a karawar mako na 29 a La Liga, wadanda suka ci mata kwallayen sun hada da Vinicius Junior mai biyu a raga da Daniel Carvajal da Brahim Diaz.

Wadanda suka ci wa Osasuna kwallayen sun hada da Ante Budimir da kuma Iker Munoz.

Da wannan sakamakon Real Madrid ta ci gaba da zama ta daya a teburin La Liga da maki 72, sai Barcelona ta biyu da maki 64, wadda ta je ta doke Atletico 3-0 ranar Lahadi.

Real din ta ci wasa 22 da canjaras daya aka doke ta fafatawa daya da cin kwallo 64 aka zura mata 20 a raga.

Kungiyar Santiago Bernabeu ce kan gaba a yawan lashe babban kofin gasar Sifaniya da 35 jimilla a tarihi.

Kuma kungiyoyi uku ne da har yanzu ke buga La Liga tun lokacin da aka fara gasar a 1928/29 da suka hada da Barcelona da Athletic Bilbao da kuma Real Madrid da ke kaka ta 54.

Barcelona ce ta fara lashe La Liga a 1928/29 daga baya Athletic Bilbao ta dauki biyu a jere daga 1930, sai Real Madrid ta fara lashe kofin a 1931/32.

Barcelona ce ke rike da kofin bara da ta lashe, wadda yanzu take ta biyu a bana, bayan saura wasa tara a karkare kakar nan.

Jerin kungiyoyin da suka lashe La Liga a tarihi

  • Real Madrid 35
  • Barcelona 27
  • Atletico de Madrid 11
  • Athletic de Bilbao 8
  • Valencia C.F 6
  • Real Sociedad 2
  • Deportivo La Coruna 1
  • Sevilla FC 1
  • Real Betis 1

Wadanda ke kan gaba a cin kwallaye a La Liga a 2023/24

Bayan da aka buga wasa 29 a La Liga, saura tara suka rage a kammala kakar bana, inda Jude Bellingham ke kan gaba a yawan cin kwallaye a Real Madrid mai 16 a raga.

Wadanda suke biye da shi sun hada da Borja Mayoral na Getafe da kuma Ante Budimir na Osasuna da kowanne yake da 15 a raga.

Wadanda ke kan gaba a zura kwallaye a La Liga

  • Jude Bellingham Real Madrid 16
  • Borja Mayoral Getafe 15
  • Ante Budimir Osasuna 15
  • Artem Dovbyk Girona 14
  • Alvaro Morata Atletico Madrid 14
  • Robert Lewandowski Barcelona 13
  • Alexander Sorloth Villarreal CF 13
  • Hugo Duro Valencia 12
  • Vinicius Junior Real Madrid 12
  • Antoine Griezmann Atletico Madrid 11
  • Gorka Guruzeta Athletic Bilbao 11

Wasannin mako na 30 da za a buga a La Liga

Juma'a 29 ga watan Maris

  • Cadiz da Granada

Ranar Asabar 30 ga watan Maris

  • Getafe da Sevilla
  • Almeria da Osasuna
  • Valencia da Real Mallorca
  • Barcelona da Las Palmas

Ranar Lahadi 31 ga watan Maris

  • Celta Vigo da Rayo Vallecano
  • Girona da Real Betis
  • Deportivo Alaves da Real Sociedad
  • Real Madrid da Athletic de Bilbao

Ranar Litinin 1 ga watan Afirilu

  • Villarre da Atletico Madrid

Saura wasa taran da suka rage a gaban Real Madrid a bana

Sauran wasa tara da suka rage a gaban Real Madrid a La Liga, wadda za ta buga karawa biyar a Santigo Bernabeu, sannan ta kai ziyara hudu a fafatawar waje.

Ranar 26 ga watan Mayu za a buga wasannin karshe na mako na 38 a babar gasar tamaula ta Sifaniya, wadda ake sa ran fayyace wadanda za su buga gasar zakarun Turai da ukun da za su yi ban kwana da La Liga.

Ana sa ran Real Madrid za ta lashe kofin tun kan a kammala fafatawar da suka rage, inda ake da sauran maki 27 a kasa.

Wasa taran da ke gaban Real Madrid a La Liga

Asabar 31 ga watan Maris din 024

  • Real Madrid da Ath Bilbao

Ranar Asabar 13 ga watan Afirilun 2024

  • Mallorca da Real Madrid

Ranar Lahadi 21 ga watan Afirilun 2024

  • Real Madrid da Barcelona

Ranar Lahadi 28 ga watan Afirilun 2024

  • Sociedad da Real Madrid

Ranar Lahadi 5 ga watan Mayun 2024

  • Real Madrid da Cadiz

Ranar Lahadi 12 ga watan Mayun 2024

  • Granada da Real Madrid

Ranar Laraba 15 Mayun 2024

  • Real Madrid da Alaves

Ranar Lahadi 19 Mayun 2024

  • Villarreal da Real Madrid

Ranar Lahadi 26 Mayun 2024

  • Real Madrid da Real Betis