Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
FA Cup: Man City da Chelsea Man United da Coventry
Mai rike da kofi, Manchester City za ta kara da Chelsea a daf da karshe a FA Cup, yayin da mai buga Championship, Coventry City za ta kece raini da Manchester United.
Coventry City ta kawo wannan matakin ne, bayan da ta yi waje da Wolverhampton a fafatawar daf da na kusa da na karshe.
Ita kuwa Manchester United ta yi nasara a kan Liverpool da cin 4-3 a karin lokaci, bayan da suka tashi 2-2 a Old Trafford ranar Lahadi.
Ita kuwa Manchester City fitar da Newcastle United ta yi a zagayen kwata fainals, yayin da Chelsea ta doke Leicester City mai jan ragama a Championship.
Dukkan wasa biyu na daf da karshe za a buga a Wembley tsakanin 20-21 ga watan Afirilu.
Rabon da Coventry ta kai zagayen na kusa da karshe tun bayan da ya lashe kofin a 1987, kuma shi ne babban kofin da take da shi a tarihi.
Tsohon dan wasan Manchester United United, Mark Robins ne ke horar da kungiyar, wanda ya dauki FA Cup a United a 1990.
Rabon da Manchester United ta dauki FA Cup mai 12 jimilla tun 2016, wadda ta yi ta biyu a kakar bara.
Mai rike da kofin Manchester City na fatan kai wa wasan karshe karo na 13 a FA Cup mai bakwai jimilla.
Chelsea kuwa ta kai zagayen karshe karo biyar daga bakwai baya a FA Cup, wadda rabon da ta lashe kofin tun 2018.