Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mbappe ya ci kwallo uku rigis karo na uku kenan a bana a PSG
Kylian Mbappe ya ci kwallo uku rigis ranar Lahadi a wasan Ligue 1 da Paris St Germain ta je ta caskara Montpellier 6-2.
Vitinha ne ya fara ci wa PSG kwallo daga baya Mbappe ya kara na biyu, kafin hutu.
Masu masaukin baki ta fara zare daya ta hannun Arnaud Nordin, sannan Teji Savanier ya farke na biyu.
Bayan da aka koma zagaye na biyu ne kyaftin din tawagar Faransa ya kara biyu, kuma na uku rigis da ya ci a fafatawa.
Sai kuma Lee Kang da Nuno Mendes kowannensu ya ci wa PSG kwallo da suka cika 6-2 da aka zura a raga a ranar Lahadin.
Kenan Mbappe ya ci kwallo 24 a Ligue 1 kawo yanzu, kuma karo na uku da ya zura uku rigis a raga a kakar nan.
Dan wasan na fuskantar kalubale kawo yanzu, bayan da PSG ke ajiye shi a benci, domin 'yan wasa su fara rayuwa ba tare da Mbappe ba mai shekara 25.
A karshen kakar nan Mbappe zai koma taka leda a Real Madrid, bayan da PSG ta amince da hakan.
Kafin nan Mbappe yana da damar lashe Champions League a PSG a karon farko, wadda za ta fuskanci Barcelona gida da waje a zagayen kwata fainals a bana.
Haka kuma yana daf da lashe Ligue 1 na hudu jimilla a kaka biyar baya, bayan da PSG ke jan ragamar teburin bana da tazarar maki 12 tsakaninta da Brest ta biyu.