Real Madrid na son Haaland, Man United da Liverpool na zawarcin Cherki

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Manchester United da Liverpool na kan gaba a zawarcin dan wasan gaba na Faransa mai taka leda a Lyon, Rayan Cherki mai shekara 21 a kakar nan. (Mail - subscription required)

Arsenal na duba yiwuwar dauko dan wasan Faransa mai taka leda a Bayern Munich Kingsley Coman, mai shekara 28. (Star)

Manchester United daTottenham na tattaunawa da Eintracht Frankfurt, kan daukar mai tsaron ragar Brazil Kaua Santos, mai shekara 21. (Bild - in German)

Chelsea na duba yiwuwar dauko mai tsaron gida na Netherland, mai shekara 33, wato Virgil van Dijk a kakar nan kafin ya rattaba hannu kan sabon kwantiragi da kungiyar Liverpool. (Mail - subscription required)

Shugaban kungiyar Real Madrid, Florentino Perez na son daukar dan wasan Manchester City, dan asalin Norway, Erling Haaland mai shekara 24. (Fichajes - in Spanish)

Liverpool na duba yiwuwar dauko dan wasan Faransa mai taka leda a Eintracht Frankfurt, Hugo Ekitike mai shekara 22 a kakar nan. (Caught Offside)

Everton ta shirya domin fafatawa da Inter Milan kan dan wasan tsakiya na Iceland, mai taka leda a Genoa, Albert Gudmundsson, mai shekara 27, wanda ke zaman aro a Fiorentina. (Teamtalk)

Ana sa ran , mai horas da kungiyar Real Madrid, Carlo Ancelotti, zai bar kulub din a karshen watan nan, bayan an gama wasan karshe na gasar Copa del Rey, inda za su kara da Barcelona, ana kuma sa ran Brazil za ta dauki dan Italiyar mai shekara 65 a aikin horas da 'yan wasanta. (Sky Sports)

Nottingham Forest na shirin fara tattaunawa kan sabon kwantiragi da dan wasan Ingila mai shekara 24, Callum Hudson-Odoi. (Football Insider)

Barcelona ta fita daga masu zawarcin dan wasan Sifaniya mai taka leda a Athletic Bilbao, Nico Williams mai shekara 22. (Marca - in Spanish)