Kafafen watsa labaran Isra'ila sun fara sukar Trump: Ko mene ne dalili?

    • Marubuci, BBC Monitoring Department
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 6

Kafofin watsa labarai na Isra'ila, waɗanda a baya suke kiran Donald Trump "babban aboki" na ƙasar, kwatsam sun sauya salon maganganunsu bayan rattaɓa hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin Amurka da Iran.

Tun daga wannan lokaci, waɗannan kafofin suka fara yin magana game da abin da suka kira "babbar cin amanar" da Trump ya yi wa Isra'ila.

Wannan sauyin ya fi bayyana a tashar Channel 14 mai ra'ayin ƴan mazan jiya, wadda ta daɗe tana goyon bayan Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu.

Masu sharhi a shirin maraice na tashar mai suna "The Patriots" sun taɓa kasancewa masu nuna goyon baya ga Donald Trump a fili, har ma da riƙe kayan da ke da alaƙa da shi yayin shiri.

Daya daga cikin masu gabatarwa, Yinon Magal, ya sha fitowa sanye da hular "Trump 2024".

A wata alama ta wannan sauyi, wani baƙo na dindindin mai suna Guy Meroz ya bayyana a shirin ranar 21 ga Yuni sanye da riga mai ɗauke da hoton Kamala Harris, wanda ya nuna adawarsa da manufofin Trump na baya‑bayan nan.

Wannan canjin na kwatsam na iya nuna wani gagarumin sauyi a goyon bayan masu ra'ayin mazan jiya na Isra'ila suke bai wa Trump a baya, da kuma dangantakar Isra'ila da Amurka baki ɗaya.

Me Channel 14 ta faɗi?

Tun bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin Amurka da Iran, masu shirye‑shiryen Channel 14 da masu sharhi suka rinƙa zargin Donald Trump da "miƙa wuya" ga Iran, suna kuma cewa ya "ci amanar gwamnatin Isra'ila."

Tal Meir, ɗaya daga cikin masu sharhi na tashar, ya shaida wa masu kallo cewa Iran ta yi wa Trump "izgilanci," kuma tana da tabbacin cewa a ƙarshe zai ja da baya.

Shirin The Patriots ya nuna wani bidiyo mai barkwanci inda Trump yake bayyana Iran a matsayin "mai hankali sosai" kuma "kyakkyawa," yayin da ake nuna hotunan Iraniyawa suna ƙona tutar Amurka.

Wani mai sharhi ya ce: "Ba a taɓa ganin shugaban ƙasa mai iko irin wannan ya yi watsi da komai gaba ɗaya kamar haka ba."

Wani kuma ya tambaya: "Me ya faru da Trump? Wa yake ba shi shawara?"

Channel 14 ta sauya daga zolaya da yin ba'a ga Trump zuwa cikakken suka a kansa a cikin dare ɗaya.

Kafin rattaɓa hannu kan wannan yarjejeniya, tashar ba ta yawan sukar Trump kai tsaye, ko da lokacin da yake matsa wa Isra'ila lamba ta dakatar da yaƙe‑yaƙe a Iran ko Lebanon.

A maimakon haka, Channel 14 ta kan kai hari ga wasu kafafen labarai da ke nuna damuwa kan matakan Trump, tana gargadin cewa zai iya ƙulla yarjejeniya da Iran a sharuɗɗan da ba su dace da Isra'ila ba.

Tashar ta kira irin waɗannan kafafe da suna "masu cin amana," tana mai cewa suna ƙoƙarin "raunana ƙasar Isra'ila."

Sai dai Channel 14—ɗaya daga cikin fitattun kafafen yaɗa labarai a Isra'ila, kuma wadda aka daɗe ana ganin tana wakiltar ra'ayoyin Netanyahu—ta sauya matsayinta kwatsam.

Sauran kafafen labarai masu ra'ayin dama ma sun bi wannan hanya.

Jaridar Makor Rishon mai tsatsauran ra'ayi wadda ke goyon bayan matsugunan Yahudawa ta zargi Trump da kasancewa "marar zurfin tunani," tana cewa Iran ba ta tattaunawa da gaskiya.

Oren Hazan, tsohon ɗan majalisar dokoki kuma baƙo na yau da kullum a tashar I24 News mai ra'ayin riƙau, ya bayyana a wannan tashar cewa Trump "mutum ne jahili wanda abin da ya fi damun sa shi ne yawan kuɗin da ke asusun bankinsa," kuma "ya kamata a ɗauke shi a matsayin wanda ba a so a Isra'ila."

Wane irin kallo ake yi wa Trump a baya?

Tun daga wa'adin mulkinsa na farko, mutane da dama a Isra'ila sun ɗauki Donald Trump a matsayin mafi kyawun shugaban Amurka da ya fi dacewa da muradun ƙasar.

Mista Trump ya amince da birnin Qudus a matsayin cikakkiyar babban birnin Isra'ila, tare da mayar da ofishin jakadancin Amurka zuwa can.

Haka kuma ya amince da ikon Isra'ila a kan tuddan Golan da aka mamaye, sannan ya janye Amurka daga yarjejeniyar nukiliyar Iran.

Lokacin da Trump ya koma kan mulki, mutane da yawa a Isra'ila sun yi zaton zai bai wa ƙasar cikakkiyar dama.

Wasu daga cikin masu ra'ayin riƙau sun nuna rashin jin daɗi lokacin da Trump ya matsa wa Isra'ila ta amince da tsagaita wuta a Zirin Gaza, amma wannan rashin jin daɗin bai fito fili sosai a tashar Channel 14 ba.

A lokacin yaƙe‑yaƙe biyu da aka yi da Iran—ɗaya a watan Yuni 2025 da ɗaya kuma a ranar 28 ga Fabrairu 2026—kafofin watsa labarai na Isra'ila sun yaba da abin da suka kira kyakkyawan haɗin kai tsakanin Amurka da Isra'ila.

Channel 14 ma ta nuna tutocin Isra'ila da na Amurka a gefe‑da‑gefe a yayin shirye‑shirye na musamman.

A lokutan da Trump ya kira Isra'ila da ta guji ƙara tsananta rikici, ko kuma lokacin da ya amince da wasu tsofaffin tsare‑tsaren tsagaita wuta da Iran ko Lebanon, Channel 14 ta yi ƙoƙarin kauce wa sukar sa kai tsaye.

Mene ne muhimmancin sabon matsayin kafafen watsa labaran?

Channel 14 ta daɗe tana kaucewa sukar Mista Trump, ko da lokacin da matakan da yake ɗauka ba su dace da abin da masu ra'ayin riƙau suke tsammani ba.

Rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da Iran ta yi alama ce ta ƙarshen amincewa ga Trump musamman ga waɗanda har yanzu suke da yakini a kansa.

Yanzu tashar, tare da sauran kafafen watsa labarai masu ra'ayin riƙau a Isra'ila, suna yin suka kai tsaye irin wanda ba su taɓa yi a baya ba.

Tashar—wadda ake ganin tana wakiltar ra'ayoyin siyasa na Benjamin Netanyahu har ma ana kiran ta "muryarsa"—na iya yiwuwa tana isar da wani matsayi da Firaministan bai bayyana a fili ba har yanzu.

A lokaci guda kuma, duba da irin farin jinin da tashar ke da shi a tsakanin masu ra'ayin riƙau, wannan sauyin na iya nuna yanayin ra'ayin jama'a a ɓangare.

Idan wannan sauyin ya ci gaba, zai iya zama alamar cewa Trump na rasa goyon baya a wajen masu ra'ayin riƙau a Isra'ila, kuma a lokaci guda, amincewar da suke da ita ga Amurka a matsayin babbar ƙawa mai aminci na raguwa.

Mene ne illar wannan sauyi da aka samu?

Wannan sauyin ya zo ne a lokacin da dangantakar Amurka da Isra'ila ke fuskantar ƙarin matsin lamba, yayin da kafofin watsa labarai na Isra'ila ke ruwaito ƙaruwar takun saƙa tsakanin Mista Trump da Mista Netanyahu.

Wata sabuwar alamar wannan taƙaddama ita ce wata tattaunawar waya mai zafi, inda aka ruwaito cewa Trump ya kira Netanyahu "mahaukaci," kuma ya hana wani shirin kai hari kan Beirut.

Daga baya, bayan hare‑haren ranar 14 ga Yuni, Trump ya ce firaministan "ba shi da masaniyar abin da yake yi ba daidai ba."

Kafofin watsa labarai na Isra'ila sun ɗauki wannan ɓaraka a matsayin wata babbar illa ga martabar ƙasar a duniya, suna rubuta cewa Isra'ila ta shiga wani zamani na "ƙasƙantanci" da ba a taɓa gani ba daga babban abokinta. Jaridar Haaretz ta rubuta cewa Mista Netanyahu na farkawa kowace rana "cikin tsananin fargaba" domin karɓar "rabonsa na kunya na yau da kullum" daga "babban abokin" Isra'ila.

Shafin Ynet ya rubuta cewa Trump ya mayar da Netanyahu "jakar bugun na Middle East."

Sai dai a ɓangaren masu ra'ayin mazan jiya, abin da suka fi karkata a kai shi ne cewa ya kamata Isra'ila ta rinƙa ɗaukar matakai da kanta, maimakon ƙoƙarin gyara dangantaka. Channel 14 ma ta jaddada buƙatar Isra'ila na ta yi aiki da kanta ba tare da dogaro ba. Wannan babban sauyi ne ga tashar da a baya take jaddada kusancin da ke tsakaninta da Trump.

Wannan bambanci na iya nuna wani zuzzurfan sauyi a tsakanin masu ra'ayin riƙau a Isra'ila, waɗanda ga alama ba sa sha'awar gyara dangantakar, kuma suna ƙara karkata zuwa ga dogaro da kai, har ma da wani tsarin ware kai daga wasu.

Da yake za a gudanar da zaɓe a wannan shekarar, wannan rikici ya kuma haifar da shakku kan ko Netanyahu zai iya ci gaba da amfani da dangantakarsa da shugabannin Amurka a matsayin muhimmin ginshiƙi na kamfen ɗinsa.

Shekaru da dama, Isra'ila ta kasance da ra'ayi ɗaya a dukkan ɓangarorin siyasa kan muhimmancin hulɗa da Washington.

Idan wannan haɗin kai ya ruguje, kuma wasu sassan al'ummar Isra'ila suka daina ganin wannan dangantaka a matsayin wajibi, sakamakon haka na dogon lokaci—cikin gida da wajen ƙasa—na iya zama mai girma sosai.