'Abu ne mai sauƙi - loƙaci ya yi da Ancelotti zai bar Real Madrid'

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Kafin wasa da Arsenal na gasar Champions League ranar Laraba a filin wasa na Bernabeu, kalma ɗaya kawai ake ji daga bakunan magaoya bayan Real ɗin - wato remontada.

Kalmar na nufin farkewa a harshen Sifaniyanci. Yayin da tawagogin Real na baya suka yi bajintar farke ƙwallayen da aka zira musu a wasanni, tawagar ta wannan karon ba ta iya yin hakan ba.

Arsenal ta doke Real 3-0 a wasan farko da suka gwabza a filin wasa na Emirates, sannan ta doke ta 2-1 a wasa na biyun, inda Saka da Martinalli suka ci mata ƙwallayen, shi kuma Vinicius Junior ya ci wa Real ɗaya.

Da wannan sakamako, Arsenal ta zama ƙungiya ta farko a tarihi da ta ci wasa biyu na farko a filin wasa na Santiago Bernabeu.

Karo na uku kenan kacal da ake fitar da Real a zagayen kwata-fayinal na gasar Champions League cikin shekara 12, kuma yanzu mai horarwa Carlo Ancelotti na sane da cewa ba za a daina magana kan rawar da shi da 'yanwasansa suka taka ba nan kusa.

"Muna da fuskar ƙoƙari da kuma ta rashin ƙoƙari," a cewar ɗan ƙasar Italiyan wanda ya fara jagorantar Madrid karo na biyu a 2021 kuma ya lashe Champions League sau uku a duka lokutan nasa.

"Mun nuna koƙarinmu a lokuta da yawa a baya, mun ci kofuna, mun ci wasanni. An fitar da mu [daga Champions League] amma akwai gasanni uku da za mu mayar da hankali a kai yanzu."

Ƙwararre kan harkokin wasanni a gasar La Liga ta Sifaniya Guillen Balague ya ce: "Real Madrid na kan wani ƙadami a yanzu. Tawagarta na neman garambawul.

"Rashin nasara a hannun Arsenal ba kawai fallasa matsala ta yi ba, tabbatar da ita ta yi. Saƙon da Ancelotti ya kamata ya fahimta a fili yake - shi ne ya bar ƙungiyar kawai."

Wane irin sauyi Real Madrid ke buƙata?

Mutane da dama za su iya cewa korar mai horarwa Ancelotti abu ne mai ɗan tsauri.

Baya ga haka, har yanzu Real ɗin na da damar kare kofinta na La Liga da ta ɗauka a bara, da kuma wasan ƙarshe da za ta buga da Barcelona a gasar Copa del Rey.

Amma bayan da ta ci Champions League na 15 da La Liga a kakar da ta gabata, babu shakka kakar bana ba ta yi mata kyau ba zuwa yanzu.

Sun yi rashin nasara a wasa 11 da suka buga a dukkan gasanni, sannan kuma wasanni biyu da suka buga da Arsenal ba su yi ƙoƙari ba.

Tuni aka fara shirin kawo sauyi a kaka mai zuwa.

Ana sa ran Trent Alexander-Arnold zai koma Madrid a kaka mai zuwa, da kuma wasu manyan 'yanwasa da ake sa ran za su bar ƙungiyar.

"Akwai buƙatar su ɗauki manyan matakai," a cewar ɗanjarida Julien Laurens. "Ko Vinicius zai ci gaba da zama? Ya za a yi da Rodrygo? Ba zai yiwu dai a ci gaba da aiki da waɗannan 'yanwasan gaban huɗu ba saboda ba za ta yi kyau ba."

Ɗanjarida Balague ma na ganin kulob ɗin na buƙatar gyara sosai kafin su iya kaiwa inda suke buƙatar zuwa.

Ya ce: "Wannan tawagar na buƙatar kuzari. Har yanzu ba a maye gurbin Toni Kroos ba, ba a riƙe ƙwallo a tsakiya. Duk da cewa Luka Modric tauraro ne har yanzu, a bayyane take ana buƙatar wani da bai kai shekara 39 ba ya kankane tsakiyar nan.

"Dole ne kulob ɗin ya ɗauki mataki sosai. Ba lallai a sabunta kwantaragin Modric da Lucas Vázquez ba. Za a iya ƙyale David Alaba ya ƙara gaba idan aka samu tayi mai ɗan kyau."