Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Zidane na nazarin komawa United, Bayern na zawarcin Rangnick
Tsohon kocin Real Madrid Zinedine Zidane na sa ido kan halin da kocin Manchester United Erik ten Hag ke ciki yayin da ake tunanin ya gwammace ya jagoranci ƙungiyar ta Old Trafford maimakon Bayern Munich. (L'Equipe)
Bayern Munich ba ta tuntubi tsohon ɗan wasan na Faransa game da zama wanda zai gaji Thomas Tuchel ba idan ya bar ƙungiyar a ƙarshen kakar wasan bana. (ESPN)
Mahukuntan Bayern Munich sun tattauna batun ɗaukar tsohon kocin ƙungiyar riƙon ƙwarya na Manchester United Ralf Rangnick, wanda shi ne mai horas da tawagar ƙasar Austria, yayin da har ila yau suke zawarcin kocin Brighton Roberto de Zerbi. (Sky Sport Germany)
Ɗan wasan tsakiya na Newcastle United da Brazil Bruno Guimaraes, mai shekara 26, ya nuna yana da niyyar ci gaba da zama a ƙungiyar a kakar wasa mai zuwa bayan ya sayi sabon gida a Arewa maso Gabashin Ingila. (Telegraph)
Manchester United za ta iya samun ƙarin fam miliyan 3.4 daga Borussia Dortmund kan kuɗin aron ɗan wasan Ingila Jadon Sancho idan ƙungiyar ta Jamus ta kai wasan ƙarshe na gasar zakarun Turai. (Times)
Ɗan wasan baya na ƙasar Netherlands Ian Maatsen, mai shekara 22, ya shaida wa Chelsea cewa yana son ya ci gaba da zama a Dortmund na dindindin bayan zaman aronsa ya ƙare. (Sky Sport Germany)
Manchester United na shirin hamayya da Atletico Madrid kan sayen ɗan wasan bayan Nice da Faransa Jean-Clair Todibo, mai shekara 24. (Mirror)
Bayern Munich na sha'awar sayen ɗan wasan Barcelona da Netherlands Frenkie de Jong, mai shekara 26, wanda ke da farashin Yuro miliyan 60-70. (Relevo)
Fulham za ta saurari tayi kan ɗan wasan Brazil Carlos Vinicius, mai shekara 29, wanda ke zaman aro a Galatasaray ta Turkiyya har zuwa ƙarshen kakar wasa ta bana. (Standard)
Ɗan wasan bayan Sifaniya Nacho, mai shekara 34, ya shaidawa Real Madrid cewa yana shirin barin ƙungiyar a ƙarshen kakar wasa ta bana. (Marca)
Nacho na iya komawa Inter Milan yayin da kulob ɗin na Italiya ya yi yunƙurin siyan shi a bazarar da ta gabata. (Football Italia)