Ban yi nadamar sayar da Palmer ba - Pep Guardiola

An wallafa

Kocin Manchester City Pep Guardiola ya ce Cole Palmer ne ya nemi ya bar ƙungiyar na shekara biyu kafin daga baya ya koma Chelsea.

City ta sayar da Palmer mai shekara 21 kan fan miliyan 42.5 a ranar rufe kasuwar 'yan wasa a Turai a watan Satumba.

Palmer ya ci kwallo 20 a Premier ya zuwa yanzu daidai da dan wasan gaban City Erling Haaland da ke son lashe wanda ya fi yawan kwallaye.

"A wasannin share fagen fara kakar wasanni, sai da nace masa ya tsaya saboda Riyad Mahrez ya tafi shi kuma ya ce a a, so nake na tafi," in ji Guardiola.

"Nayam kaka biyu ta wasanni, me zan iya cewa?

Palmer ya ci kwallo hudu a wasan da suka cinye Everton a ranar 15 ga watan Afrilu abin da ya kai yawan kwallayen da ya ci zuwa 20 a wannan kakar, kuma yanzu zai fafata da tsohuwar ƙungiyarsa a wasan kusa da daf da na ƙarshe a FA a ranar Asabar.

Yana daf da lashe dan wasan da ya fi kowanne ƙoƙari a FA kuma yanzu ya samu shiga cikin tawagar kocin Ingila Gareth Southgate da za ta buga Euro 2024.

Koƙarin da ya fara ya janyo tambayoyi masu yawa daga mutane kan cewa duk da kwarewar Pep amma ya kyale Palmer ya bar ƙungiyar.

Kocin ya ce gaskiyar lamari shi ne ba zai iya ci gaba da riƙe dan wasan ba a City.

"Ya nemi ya bar ƙungiyar na kaka biyu," in ji Guardiola. "Na ce a a ka tsaya,. Me kuma zan iya yi bayan haka?"

A 2021 Palmer ya sanya hannu kan kwantaragin shekara biyar da City.

A wannan lokacin wasa biyu kawai ya buga wa ƙungiyar.

Wasa uku kawai aka fara da shi a gasar Premier da yana City, kuma Guardiola ya masa cewa hakan watakila bai wadaci ɗan wasan ba.

"Na fada a lokuta da dama watakila ban ba shi lokacin da yake so ba kuma buƙata, yanzu kuma yana samun irin wannan lokacin a Chelsea," in ji shi.

Kocin Chelsea Mauricio Pochettino ya ce yana godiya ga Chelsea da ta kyale Palmer ya koma ƙungiyar, "Damar da aka ba shi ta koma wa wata kungiyar" yana yawan godiya kan tshuwar ƙungiyarsa.

"Ko da yaushe yana yawan magana kan su da Pep," in ji Pochettino.