An tsayar da ranar El Clasico tsakanin Real da Barca a La Liga

Asalin hoton, Getty Images
An tsayar da ranar da za a buga wasan hamayya na El Clasico a gasar La Liga tsakanin Real Madrid da Barcelona wasan farko a kakar nan.
Tuni mahukuntan babbar gasar tamaula ta Sifaniya ta tsayar da ranar 16 ga watan Oktoba, domin fafatawar tsakanin manyan kungiyoyin tamaula biyu na kasar.
Karawar za ta zama ta mako na tara da Real Madrid za ta karbi bakuncin kungiyar Camp Nou a gumurzun da za su yi a Santiago Bernabeu.
Bayan da aka buga wasan mako na shida a La Liga, Real Madrid ce ta daya a kan teburi mai maki 18, wadda ta lashe dukkan karawar da ta yi a bana.
Barcelona ce ta biyu da tazarar maki biyu tsakaninta da Real Madrid, bayan da ta buga canjaras a wasan makon farko da Rayo Vallecano.
El Clasico na bana zai kara jan hankalin 'yan kallo, bayan da Barcelona ta sayo 'yan wasa da yawa a bana.
To sai dai ana ganin za a buga wasan na hamayya tsakanin Karim Benzema da Robert Lewandowski, wadanda suka yi kaurin suna wajen zura kwallaye a raga.
Benzema ne ya lashe kyautar takalmin zinare a Sifaniya a bara, shi kuwa Lewandowski, wanda ya koma Barca a bana daga Bayern Munich, shi ne kan gaba da takwas a raga a La Liga.
To sai dai watakila Real Madrid ta amfana da wasan, bayan da masu tsaron Barcelona biyu ke jinya da ya hada da Jules Kounde da kuma Ronald Araujo.
Kungiyoyin biyu sun kara sau uku a bara
2021/2022
Spanish La Liga Lahadi 20 ga watan Maris 2022
• Real Madrid 0 - 4 Barcelona
Spanish Super Cup Laraba 12 ga watan Janairu 2022
• Barcelona 2 - 3 Real Madrid
Spanish La Liga Lahadi 24 ga watan Oktoban 2021
• Barcelona 1 - 2 Real Madrid
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wasannin da Real Madrid za ta buga kafin El Clasico
Spanish La Liga Lahadi 2 ga watan Oktoba
• Real Madrid da Osasuna
Champions League Laraba 5 ga watan Oktoba
• Real Madrid da Shakhtar
Spanish La Liga Asabar 8 ga watan Oktoba
• Getafe da Real Madrid
Champions League Talata 11 ga watan OOktoba
• Shakhtar da Real Madrid
Spanish La Liga Lahadi 16 ga watan Oktoba
• Real Madrid da Barcelona
Wasannin da Barcelona za ta yi kafin ta je Santiago Bernabeu
Spanish La Liga Asabar 1 ga watan Oktoba
• Mallorca da Barcelona
Champions League Talata 4 ga watan Oktoba
• Inter da Barcelona
Spanish La Liga Lahadi 9 ga watan Oktoba
• Barcelona da Celta Vigo
Champions League Laraba 12 ga watan Oktoba
• Barcelona da Inter
Spanish La Liga Lahadi 16 ga wata Oktoba
• Real Madrid da Barcelona










