Real za ta san wadanda za ta fuskanta a Champions League na bana

Asalin hoton, Getty Images
Ranar Alhamis 25 ga watan Agusta za a raba jadawalin Champions League kakar 2022/23 da za a yi a Istambul, Turkiya.
Karo na 68 da za a gudanar da babbar gasar tamaula ta kungiyoyin zakarun Turai, karo na 31 tun bayan da aka sauya fasalin wasannin.
Za a fara gumurzun cikin rukuni a UEFA Champions League daga ranar 6 ga watan Satumba zuwa 10 ga watan Yunin 2023.
Real Madrid ce mai rike da kofin da ta lashe a kakar da ta wuce, bayan doke Liverpool a Faransa, ta dauki na 14 jumulla.
Za a raba jadawalin kungiyoyi 32, sannan a fara wasannin cikin rukuni daga nan a fada zagaye na biyu har zuwa daf da na kusa da na karshe, sai karawar daf da karshe da kuma ta karshe.
Yadda za a raba jadawalin wasannin cikin rukuni a Champions League
Kungiyoyi 32 ne za su fafata a kakar bana, 26 suka samu tikitin buga wasannin kai tsaye da kuma shida da suka yi karawar cike gurbi.
Za a raba kungiyoyin zuwa kashi hudu, inda tukunyar farko za ta kunshi mai rike da kofin wata Real Madrid da Zakarun shida da suka lashe kofin gasarsu daga fitattun kasahen da ke kan gaba a tamaula, wadanda ba su samu shiga wasannin bara ba.
Za a samu kungiyoyi a tukunya ta biyu zuwa hudu kan darajar da suke da ita a fagen taka leda a Turai, kamar yadda humumar Turai kan fitar da jadawalin kwazonsu.
Ba kungiyar da za ta kara da wadda suke kasa daya a cikin rukuni- za a sanar da wasu dokokin kan wasa tsakanin 'yan kasa daya a lokacin bikin raba jadawalin.

Asalin hoton, UEFA
Me zai faru idan an kammala raba jadawalin?
Da zarar an kammala raba jadawalin za a fayyace ranakun da za a fara wasannin cikin rukuni da lokacin da za a karkare gasar ta kakar nan.
Kungiyoyi biyu daga kowanne rukuni za su kai wasan zagaye na biyu da zai kunshi kungiyoyi 16.
Wadanda suka yi na uku a rukunnai za su koma buga gasar UEFA Europa League, domin fuskantar wadanda suka zama zakaru a karawar gasar zakarun Turai mai daraza ta biyu.
Wadanne ranakun za a buga wasannin cikin rukuni a Champions League?
Wasannin farko: Ranar 6/7 ga watan Satumba
Wasanni na biyu: Ranar 13/14 ga watan Satumba
Wasanni na uku: Ranar 4/5 ga watan Oktoba
Wasanni na hudu: Ranar 11/12 ga watan Oktoba
Wasanni na biyar: Ranar 25/26 ga watan Oktoba
Wasanni na shida: Ranar 1/2 Nuwamba
Wasannin zagaye na biyu: Ranar 7 ga watan Nuwamba
Ranakun da za a fara wasannin zagaye na biyu a Champions League

Asalin hoton, Getty Images
Wasannin zagaye na biyu: Daga ranakun 14/15/21/22 Fabrairun 2023, sannan
Wasa na biyu daga ranakun: 7/8/14/15 ga watan Maris 2023
Quarter-finals: Daga ranakun 11/12 da zagaye na biyu ranar 18/19 Afirilun 2023
Daf da karshe: Daga ranakun 9/10 zagaye na biyu ranar 16/17 ga watan Mayun 2023
Wasan karshe: Ranar 10 ga watan Yunin 2023
A ina ne za a buga wasan karshe a Champions League kakar 2023?
Za a buga karawar karshe a filin wasa na Ataturk a Istambul, filin da tawagar Turkiya ke buga wasanninta.
Filin ne ya karbi bakuncin wasan karshe a 2005, wanda AC Milan ta ci Liverpool 3-0 daga baya kungiyar Anfield ta farke ta lashe kofin.
Tun farko an tsara cewar filin ne zai karbi bakuncin karawar karshe a 2020 daga baya aka mayar da wasan Lisborn, sakamakon bullar cutar korona.
An kara tsara cewar filin ya karbi bakuncin fafatawar karshe a 2021 a Istambul, nan ma aka mayar da wasan Porto, saboda dokar hana yada cutar korona.









