'Na ji takaicin sakin wadanda suka min fyaɗen taron dangi da kashe min 'yan uwa'

Bilkis ta ce tana so azzaluman da suka kai mata hari su fahimci girman abin da suka aikata
Bayanan hoto, Bilkis ta ce tana so azzaluman da suka kai mata hari su fahimci girman abin da suka aikata
An wallafa

Bilkis Bano, wadda wani dandazon 'yan ƙabilar Hindu suka yi wa fyaɗe tare da kashe 'yan uwanta 14 yayin zanga-zangar nuna tsanar Musulmai a 2002 a Jihar Gujrat ta Indiya, labarinta ya sake dawowa kafofin yaɗa labarai.

A ranar Litinin ne mutum 11 da aka yanke wa ɗaurin rai-da-rai kan laifin fyaɗe da kisan kai game da abin da aka yi wa Bilkis suka fito daga gidan yarin, har ma aka yi musu tarɓa ta girmmawa.

Ciin wani bidiyo da tuni ya karaɗe shafukan zumunta, an ga mutanen jere a bakin gidan yarin Godhra 'yan uwansu na raba musu alawa da kuma taɓa ƙafafuwansu don nuna girmamawa.

Cikin wata sanarwa cikin dare da fitar, Bilkis ta kira matakin sakin mutanen "rashin adalci" kuma ta ce lamarin "ya girgiza ta" game da neman adalci.

"Lokacin da na ji cewa mutanen da suka ɗaiɗaita dangina sun fito daga gidan yari, sai na rasa ma abin da zan ce. Har yanzu ba ni da ta cewa," a cewarta.

"Ta yaya za a dinga yi wa mata masu neman adalci irin wannan? Na yarda da manyan kotunanmu. Na amince da tsarin kuma har ma na fara haƙurƙurtar da kaina game da baƙin cikin. Sakin waɗannan ɗaurarrun ya hargitsa ni kuma ya sa na daina yarda da tsarin shari'a," kamar yadda ta rubuta.

Ta nemi gwamnatin Gujrat ta "dakatar da wannan zalincin" kuma "ta dawo min da 'yancina na rayuwa ba tare da fargaba ba".

Wannan maƙalar na ƙunshe da labaran da ka iya tayar wa masu karatu hankali.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A ranar Litinin gwamnatin Gujrat ta sanar da sakin ɗaurarrun yayin da Indiya ke bikin cikarta shekara 75 da samun 'yancin kai.

Wani babban jami'in gwamnati ya ce an saki mutanen - waɗanda aka ɗaure tun a 2008 - bayan wani kwamati ya duba wasu abubuwa ciki har da shafe sama da shekara 14 a gidan yari da kuma shekarunsu da ɗabi'unsu a gidan yarin.

Matakin da jam'iyyar Bharatiya Janata Party (BJP) ta 'yan ƙabilar Hindu ta ɗauka - wadda ita ce mai mulki a ƙasar - ya haifar da ɓacin rai a Indiya.

m'iyyun adawa sun yi Allah-wadai da shi. 'Yan gwagwarmaya da 'yan jarida duka sun bayyana matakin da wanda bai dace ba a kan Musulman Indiya 'yan tsiraru.

An yi ta kai wa Musulmai hare-hare tun bayan da BJP ta hau mulki a 2014. Wasu da dama na cewa sakin nasu ya saɓa wa shawarwarin da gwamnatin tarayya da ta Jihar Gujrat suka bayar. Dukkansu sun ce ba zai yiwu a yafe wa mutanen da aka ɗaure ba kan laifin fyaɗe da kisan kai ba.

Akasari akan zartar da hukuncin ɗaurin rai-da-rai ne ko kuma kisa kan irin waɗannan laifuka a Indiya.

Sai dai Bilkis da danginta ne lamarin ya shafa a yanzu.

An fara far wa Musulmai ne bayan an cinna wa wani jirgin ƙasa na fasinja wuta a Godhra da ya kashe 'yan addinin Hindu 60 masu ibada

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An fara far wa Musulmai ne bayan an cinna wa wani jirgin ƙasa na fasinja wuta a Godhra da ya kashe 'yan addinin Hindu 60 masu ibada

Harin da aka kai wa Bilkis da danginta na cikin mafiya muni a lokacin, wanda ya fara bayan 'yan addinin Hindu masu ibada 60 sun mutu a wata wuta da ta tashi a kan jirgin ƙasa a garin Godhra.

Bayan sun zargi Musulmai da cinna wutar, wasu matasan Hindu sun far wa unguwannin Musulman. Mutum fiye da 1,000 aka kashe cikin kwana uku, akasarinsu Musulmai.

Firaminista Narendra Modi, wanda shi ne babban ministan Gujarat a lokacin, ya sha suka kan yadda ya gaza ɗaukar matakin da ya kamata don kare rayuka. Ya sha musanta aikata ba daidai ba kuma bai taɓa neman afuwa ba.

A 2013, wani kwamatin Kotun Ƙoli ya ce babu wata cikakkiyar hujja da za a iya tuhumar sa. Amma masu bin sawun lamurra sun ci gaba da zargin sa game da hargitsin da ya faru a lokacin gwamnatinsa.

Tsawon shekaru, kotuna sun ɗaure mutane da dama kan hargitsin amma manya daga cikinsu sun samu beli ko kuma wasu manyan kotuna sun wanke su. Cikinsu har da Maya Kodnani, tsohon minista kuma mataimaki na musaman ga Modi, wanda wata kotu ta bayyana shi da "jagoran rikicin".

Yanzu kuma an sake sakin mutanen da suka zalinci Bilkis.

Na haɗu da Bilkis Bano a watan Mayun 2017 a wani gidan ɓuya a birnin Delhi, 'yan kwanaki bayan kotu ta tabbatar da ɗaurin rai-da-rai ga mutanen 11.

Tana tsaka da hawaye, ta ba da labarin harin.

Mutum sama da 1,000 aka kashe a Gujarat akasarinsu Musulmai tsawon kwana uku a 2002

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mutum sama da 1,000 aka kashe a Gujarat akasarinsu Musulmai tsawon kwana uku a 2002

A safiyar da ta biyo bayan gobarar jirgin, Bilkis - mai shekara 19 a lokacin ɗauke da cikin yaronta na biyu - ta kai ziyara wajen iyayenta a wani ƙauye da ake kira Randhikpur da ke kusa da Godhra tare da 'yarta mai shekara uku.

"Ina cikin madafi ina dafa abincin rana, lokacin da innata da 'ya'yanta suka shigo a guje. Suka ce an kunna wa gidansu wuta kuma dole su fice nan take," kamar yadda ta faɗa min. "Mun gudu da iya kayan da suke jikinmu, babu lokacin da ma za mu saka takalmi."

Bilkis na cikin rukunin Musulmai 17, da 'yarta da mahaifiyarta da 'yar uwarta mai cki da ƙannenta da 'ya'yan 'yan uwanta maza da mata, sai kuma wasu maza manya biyu.

Sun yi ta yawon neman mafaka tsawon kwanaki a ƙauyuka da masallatai ko kuma a wajen mutanen kirki daga cikin 'yan Hindu.

Da safiyar 3 ga watan Maris yayin da suke kokarin tafiya wani ƙauye da suke ganin za su zauna lafiya, rukunin wasu maza ya tare su.

"Sun kai mana hari da takubba da sanduna. Ɗaya daga cikinsu ya ƙwace 'yata kuma ya jefar da ita a ƙasa tare da haɗa kanta da wani dutse."

Azzaluman maƙwabtanta ne a ƙauyen, waɗanda ta saba gani a kusan kullum tana yarinya. Suka yayyaga kayan jikinta kuma suka yi mata fyaɗe, duk da irin roƙon su da ta dinga yi na su yi mata afuwa.

Ita ma wata 'yar 'yar uwarta da ta haihu 'yan kwanakin da suka wuce yayin da suke gudun hijira, aka yi mata fyaɗe, aka kashe ta, aka kashe jaririn nata.

Bilkis ta tsira da ranta ne saboda ta sume kafin azzaluman su tafi suna tsammanin ta mutu.

Yara maza biyu - mai shekara bakwai da kuma huɗu - su ne kaɗai sauran waɗanda suka tsira daga kisan gillar.

Firaminista Modi ne babban ministan Gujarat lokacin da aka kashe Musulmai a zanga-zangar tsana a 2002

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Firaminista Modi ne babban ministan Gujarat lokacin da aka kashe Musulmai a zanga-zangar tsana a 2002

A bayyana take ƙarara cewa wasu 'yan sanda da kuma jami'an gwamnati sun yi yunƙurin tilasta mata.

An lalata hujjoji sannan an binne waɗanda aka kashe ba tare da wani gwaji ba. Likitocin da suka yi mata gwaje-gwaje sun ce ba a yi mata fyaɗe ba amma an sha yi mata barazanar kisa.

Har sai a 2004 aka fara kama mutane game da lamarin bayan Kotun Ƙoli ta mayar wa gwamnatin tarayya da batun. Sannan babbar kotun ta ce kotunan Gujarat ba za su iya yi mata adalci ba, abin da ya sa aka mayar da ƙarar zuwa birnin Mumbai.

Kazalika, shari'ar tata ta haddasa wa daginta hijira iri-iri, har sai da suka sauya gida sau aƙalla 12.

"Har yanzu ba za mu iya komawa gida ba saboda a tsorace muke. 'Yan sanda da gwamnati kullum taimaka wa azzaluman suke yi. Lokacin da muke Gujarat dole muka dinga rufe fuskokinmu, muka daina ba da adireshinmu."

Lokacin da ake yin shari'ar, an yi ta kiran a yanke wa maharan hukuncin kisa. Amma bayan kotun Mumbai ta ɗaure su ra-da-rai, ta faɗa min cewa "ba ramuwa ce a gabanta ba", kawai dai tana son "su fahimci girman abin da suka aikata mata ne".

"Ina fatan wata rana za su gane girman laifinsu, yadda suka kashe ƙananan yara da kuma yi wa mata fyaɗe."

Amma ta ce tana son su ƙare rayuwarsu a gidan yari".

A ranar Talata Mr Rasool ya faɗa wa jaridar Indian Express cewa matarsa "na cikin damuwa da takaici".

"Yaƙin neman adalci da muka dinga yi ya tashi a banza a lokaci guda," a cewarsa.

"Ba mu da lokacin da za mu zauna tunanin wannan labari don mun san ɗaurarrun sun koma gida ma yanzu."