'An kai wa tawagar Atiku Abubakar hari a Maiduguri'

Atiku Abubakar

Asalin hoton, Twitter/@Atiku

An wallafa

Rahotanni daga jihar Borno a Najeriya na cewa wasu matasa sun kai wa jerin-gwanon motocin ɗan takaran shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar hari.

An kai harin ne a lokacin da motocin ke kan hanya zuwa dandalin taro na Ramat Square da ke birnin na Maiduguri, domin yi wa magoya bayansa jawabi.

Farmakin ya yi sanadiyyar farfasa wasu motocin da ke cikin jerin gwanon, haka nan wasu bayanai na cewa akwai mutane da aka raunata.

A wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta, an ga motoci da dama na yaƙin neman zaɓen Atikun waɗanda aka fasa gilasan su. 

Babbar Jam'iyyar adawa a Najeriya ta PDP ta yi Allah wadai da harin da ta ce wasu ɓata garin siyasa ne suka kai mata a yayin yaƙin neman zaben da take yi a birnin Maidugurin.

PDP ta ɗora alhakin wannan hari kan gwamnatin APC Jihar Bornon. 

Rahotanni sun bayyana cewa sama da mutum 70 aka raunata a yayin harin sa'nnan baya ga motoci da aka lalata da ƴan jam'iyyar. 

Sai dai a nata bangaren gwamnatin Jihar Borno ta bakin kakakinta Isa Gusau, ta musanta zargin da PDP ke yi mata inda hasali ma ta ce watakila PDP ce ta shirya harin.

Hare-hare kan ayari ko kwambar motocin yakin neman zabe musamman idan an kada gangar siyasa ba sabon abu bane a Najeriya inda aka sha tafka asarar rayuka da dukiyoyi sakamakon wannan lamari.

Ƴan sanda sun musanta cewa an kai wa Atiku hari

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ƴan sanda a jihar Borno sun musanta cewar an kai wa ayarin motocin ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP hari lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa dandalin Ramat domin yi wa magoya bayansa jawabi.

Mai magana da yawun rundunar a jihar Borno, ASP Kamilu Shatambaya lokacin da ya gana da manema labaru, ya ce zargin kai wa ayarin motocin Atiku Abubakar hari shaci-faɗi ne kawai.

Shatambaya ya ce Atiku Abubakar ya samu rakiyar jami’an tsaro zuwa fadar Shehun Borno da kuma lokacin da ya tafi dandalin taro na Ramat domin ganawa da magoya bayansa.

Ya ƙara da cewa “Kwamishinan ƴan sanda na jihar Mr Abdu Umar ya halarci wurin taron domin tabbatar da cewa an gudanar da taron lami lafiya.”

Ya ce “mun kuma zagaya asibitoci domin ganin ko da gaske ne an kwantar da mutane 74 a asibiti, amma babu kowa ba.”

Sai dai ya ce an kama wani mutum mai suna Danladi Abbas saboda yunƙurin da ya yi na jifan ayarin motocin ɗan takaran a kan hanyar filin jirgin sama na Maiduguri.