Van Dijk ya tsawaita zamansa a Liverpool

Asalin hoton, Getty Images
Kyaftin ɗin Liverpool Virgil van Dijk ya sanya hannu kan sabuwar yarjejeniya tsakaninsa da ƙungiyar.
Tsohon kwantaragin ɗan ƙasar Netherlands ɗin mai shekara 33 zai ƙare ne a ƙarshen wannan kakar.
Yanzu ɗanwasan bayan ya bi sawun Mohamed Salah, wanda ya sanya hannu kan yarjejeniyar shekara biyu a makon da ya gabata.
"Da ma kodayaushe Liverpool ce [a raina]," a cewar Van Dijk da aka dinga alƙantawa da komawa Paris St-Germain.
"Abin da ya faru kenan. Abin da ke cikin zuciyata kenan, tsarin kenan da ma."
Van Dijk wanda ya buga wa Liverpool wasa 314, an naɗa shi kyaftin a 2023 bayan Jordan Henderson ya bar kulob ɗin.
"Babu wata tantama a raina cewa ba a nan zan ci gaba da taka leda ba ni da iyalina," kamar yadda Van Dijk ya bayyana.
Van Dijk ya koma Liverpool kan fam miliyan 75 daga Southampton a watan Janairun 2018.
Tun daga lokacin ne kuma ya taimaka wa Liverpool lashe kofin Premier ɗaya, da Champions League, da FA Cup, da Club World Cup, da EFL Cup biyu.











