Man Utd na Harin Adeyemi, Chelsea na son Julian Alvarez

.

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Manchester united na son ɗaukar Karim Adeyemi a watan Janerun mai zuwa, Chelsea na harin Julian Alvarez, Liverpool da Tottenham na harin Antoine Semenyo.

Manchester United na duba yiwuwar ɗauko ɗan wasan gaban Borussia Dortmund da Jamus Karim Adeyemi, 23. (Bild - in German, subscription required)

Chelsea na shirye-shiryen rattaba hannun kan siyen Julian Alvarez, 25, ɗan wasan gaba na Atletico Madrid a kakar wasa ta gaba kan Euro miliyan 150 (£132m). (Fichajes - in Spanish)

Manchester United na harin ɗan wasan tsakiya na Brazil da Wolves Joao Gomes, 24, a wani yuƙuri da suke yi na ƙara ƙarfafa gurbin lamba shidan su. (Mail - subscription required)

Liverpool da Tottenham na neman ɗan wasan gaba na Ghana da Bournemouth Antoine Semenyo, 25, don ƙara ƙarfafa kai harin ƙwallo. (Teamtalk)

Ɗan wasan tsakiya na Ingila James Garner, 24, ya ce babu wani bayani ko tattunawa da ya ke yi da Everton kan tsawaita kwantaraginsa, da za ta ƙare a kaka mai zuwa. (FourFourTwo)

Newcastle United, ta matsu ta ɗauko ɗan wasan tsakiya na Jamus da AZ Alkmaar, Kees Smit mai shekaru 19, wanda Barcelona, da Bayern Munich, da Borussia Dortmund da Real Madrid ke nema su ma. (Mail - subscription required)

West Hamta sake nuna sha'awarta na ɗaukar ɗan wasa baya na Toulouse Charlie Cresswell, da ya buga wa tawagar ƙungiyar ƙwallaon kafa ta ƙasar Igila yan shekaru 21 wasa. (Talksport)

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Brentford, da Everton da Leeds, na rige-rigen ganin sun dauki ɗan wasan gaban Celtic da ke Scotland Daizen Maeda, 28, a watan Janeru. (Teamtalk)

Roma na son ɗaukar ɗan wasan gaban Netherlands Joshu Zirkzee, a masatyin aro daga Manchester United a watan Janeru, sai dai sun fusktanar gogayya daga Everton, da West Ham, da Juventus da PSV Eindhoven. (Mirror)

Manchester United na son siyen mai tsaron ragar Malomo da ke Swedin, Melker Ellborg, 22, a matsayin shirin ko ta kwana ga mai tsaron ragar ƙungiyar Senne Lammens, 23. (Sun)

Dan wasan baya na Ingila da Manchester United Harry Amass, 18, ya shorya ci gaba da zama a msatyin ɗan wasan aro, a Sheffield Wednesday, har bayan kakar siyeen ƴan wasa. (Express)

Wolfsburg ta ƙyala ido akan ɗan wasan gaban jamus da West Ham Niclas Fullkrug, 32, ɗan mai tsaron gida na Brentford Kristoffer Ajer. (Sky Sports News)

Mai horar da yan wasan Brazil Carlo Ancelotti, ya musanta cewar ya shiadawa ɗan wasan gaba na Real Madrid Endrick, da ke shirin koma wa Lyon a masatyin aro, sai ya bar ƙungiyar Spaniyar idan har yana son shiga cikin ƴan wasan da za su buga gasar kofin duniya na 2026. (AS - in Spanish)

Ɗan wasan baya na Ecuador Willian Pacho, 24, ya sanya hannu kan tsawaita kwantaraginsa da Paris St-Germain zuwa 2030. (RMC Sport - in French)