Bellingham na son Madrid amma Liverpool za ta yi masa tayi, Newcastle za ta yi cefane

An wallafa

Matashin dan wasan tsakiya na Ingila Jude Bellingham, mai shekara 19, zai tattauna maganar tafiyarsa da Borussia Dortmund bayan da ya nuna wa Real Madrid cewa ya fi son tafiya Sifaniya maimakon gasar Premier. (Mirror)

Sai dai duk da haka Liverpool, har yanzu tana da kwarin guiwa cewa za ta sayi dan wasan kuma za ta lasa masa zuma a baki ta nuna masa damar ba zama sabon Steven Gerrard' a Anfield. (Florian Plettenburg, Sky Germany)

Brighton ta yi watsi da tayin fam miliyan 55 da Chelsea ta gabatar mata na sayen dan wasanta na takiya Moises Caicedo dan Ecuador mai shekara 21 (Athletic)

Newcastle ta jera sunayen 'yan wasa tara da take son saye, wadanda suka hada da dan gaban Everton na tawagar 'yan kasa da shekara 21 ta Ingila Anthony Gordon, da 'yan wasa uku na Chelsea: dan gaban Moroko, Hakim Ziyech, da dan wasan tsakiya na Ingila Conor Gallagher da kuma Ruben Loftus-Cheek. (Telegraph) 

Dan gaban Wolves Goncalo Guedes, mai shekara 26, ya tafi kasarsa Portugal kafin ya je ya kammala shirin tafiya aro da zai yi zuwa Benfica(Matteo Moretto )

Everton na tuntubar Rennes a kan matashin dan wasanta Kamaldeen Sulemana na tawagar Ghana. (Givemesport)

Wolves ta amince ta sayi dan bayan West Ham Craig Dawson na Ingila a kan fam miliyan 3.3 (Independent)

Arsenal na sha'awar sayen dan gaba na gefe na Bournemouth Jaidon Anthony na Ingila, a kokarin da Arteta ke yi na kara yawan 'yan wasansa. (Mail)

Dole ne Gunners din su tabbatar da kammala cinikin Leandro Trossard daga Brighton zuwa karfe 12:00 na rana agogon GMT , ranar Juma'ar nan, muddin suna son dan wasan gaban na Belgium ya buga musu wasansu na gaba ranar Lahadi, da Manchester United. (Mirror)

A shirye Chelsea take ta yi gogaya da Tottenham a kan neman golan Brentford da Sifaniya David Raya, yayin da Tottenham din kuma ke son sayen golan Slovenia Jan Oblak, na Atletico Madrid. (Evening Standard)

Crystal Palace ba ta da shirin rasa 'yan wasanta biyu a bazaran nan ba- matashin dan wasan Faransa Michael Olise, mai shekara 21, da kuma dan Ivory Coast Wilfried Zaha.(Mail)

Leicester na harin dan bayan Stoke City Harry Souttar kuma tuni ta gabatar da tayin fam miliyan 10 a kan dan Australiar. (GianlucaDimarzio.com)

Newcastle  ta gabatar wa da Flamengo tayin fam miliyan 14 a kan matashin dan wasanta na tsakiya dan Brazil Matheus Franca. (Fabrizio Romano)