Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Manchester City ta farfado ta kwaci kanta a hannun Tottenham da ci 4-2
Manchester City ta yunkuro ta nuna wa Tottenham cewa ruwa ba sa'an kwando ba ne a karawar da suka yi a filin Etihad, inda masu masaukin bakin suka rage tazarar da ke tsakaninsu da ta daya a teburin Premier, Arsenal zuwa maki biyar.
Da farko dai alamu sun nuna Spurs din na yi wa abokan hamayyarsu na arewacin London, wato Arsenal rana, lokacin da suka zura wa Man City kwallo biyu ba ko daya a raga ana shirin tafiya hutun rabin lokaci.
Hakan ya sa ake ganin kamar City din ta kama hanyar rashin nasara karo na uku a jere.
Dejan Kulusevski na fara dag ragar masu masaukin bakin a minti na 44, sai kuma Emerson Royal ya kara ta biyu da ka ana dab da tafiya hutun rabin lokaci.
Al'amarin bai yi wa magoya bayan City dadi ba, to amma kungiyar ba ta karaya ba inda ta samu kwarin guiwa daga irin jajircewar Riyad Mahrez, abin da ya kai ta ga zazzaga kwallaye har uku a cikin minti 12.
Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci ne Álvarez ya rama kwallo daya, a minti na 51 sai kuma Haaland ya ci wa City ta biyu minti biyu tsakani.
A minti na 63 ne kuma sai Mahrez ya farke ta uku, an kama hanyar kammala wasan ne a minti na 90 sai ya sake zura ta hudu, inda suka tashi da ci 4-2.
Da wannan sakamako Arsenal ta ci gaba da jan ragamar gasar ta Premier da maki 47 a wasa 18, yayin da Manchester ke bi mata baya da maki 42 amma kuma ita a wasa 19.
Manchester United ita ce ta uku a teburin da maki 39 a wasa 19, yayin da New Castle ke zaman ta hudu da maki 38 a wasa 19.