Barcelona ta doke Atletico Ceuta da ci biyar da nema

An wallafa

Barcelona ta lallasa Atletico Ceuta a gasar kofin Copa del Rey da ci biyar da nema inda ta tsallake zuwa zagaye na gaba.

Rafinha ne ya soma ci wa Barca kwallo kafin a tafi hutun rabin lokaci. Daga bisani Lewandowski ya zura kwallo biyu, Ansu Fati ya ci daya sai kuma Kessie da ya zura kwallo daya ana sauran minti 13 a tashi wasan.

Wannan shi ne karo na uku da Barcelona ta fuskanci Ceuta, wanda a baya a 2010 kungiyar Camp Nou ta yi nasara da ci 7-2 gida da waje.

Barcelona ta dauki kofin farko a bana, bayan da ta ci Real Madrid 3-1 ranar 15 ga watan Janairu ta dauki Spanish Super Cup na 14 jumulla a Saudi Arabia.

Barcelona tana matakin farko a kan teburin La Liga a kakar nan mai maki 41 da tazarar maki uku tsakaninta da Real Madrid ta biyu.