Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Casemiro ba zai buga wasan Arsenal ba bayan karbar katin gargadi na biyar
Crystal Palace da Manchester United sun tashi 1-1 a kwantan wasan mako na bakwai a gasar Premier da suka kara ranar Laraba a Selhurst Park.
Bruno Fernandes ne ya ci wa United kwallo daf da za su je hutu, inda Palace ta farke ta hannun Michael Olise daf da za a tashi daga wasan.
To sai dai kuma a karawar an bai wa dan wasan United, Casemiro katin gargadi, bayan da ya yiwa Wilfred Zaha keta a minti na 80.
Hakan na nufin dan kasar Brazil ya karbi katin gargadi na biyar jumulla, kenan ba zai yi wa United wasan Premier da Arsenal a Emirates ranar Lahadi ba.
''A wasan farko mun doke su ba tare da Casemiro ba, ya kamata mu kara yin hada,'' in ji dan kwallon.
Arsenal ce ta daya a teburin Premier da tazarar maki takwas tsakaninta da Manchester City ta biyu, kuma United ce kadai ta doke ta 3-1 a bana a Old Trafford.
Casemiro ya shiga wasan na Arsenal saura minti 10 a tashi daga karawar a lokacin da United ta kammala zura kwallayenta a raga.
Wasa daya kacal aka ci United a karawa 20 a dukkan fafatawa tana ta ukun teburi da maki 39 iri daya da na Manchester City ta biyu.
Wasa biyar da aka bai wa Casemiro katin gargadi a Premier
- Man Utd 0 – 0 Newcastle Lahadi 16 ga watan Oktoban 2022
- Man Utd 2 – 0 Tottenham Laraba 19 ga watan Oktoban 2022
- Wolves 0 – 1 Man Utd Asabar 31 ga watan Disambar 2022
- Man Utd 2 – 1 Man City Asabar 14 ga watan Janairun 2023
- Crystal Palace 1 – 1 Man Utd Laraba 18 ga watan Janairun 2023