An bai wa Ramos jan kati na 28 a tarihin sana'arsa ta tamaula

Red Card

Asalin hoton, Reuters

An wallafa

An bai wa Sergio Ramos jan kati karo na 28 a tarihin sana'arsa ta kwallon kafa a wasan da Paris St-Germain ta buga da Stade de Reims.

Ranar Asabar PSG ta ziyarci Reims a wasan mako na 10 a gasar Ligue 1 da suka tashi 0-0.

Tun kan hutu aka bai wa tsohon dan wasan Real Madrid kati biyu na gargadi, hakan ya sa aka yi masa jan kati.

PSG ta buga wasan ba tare da Lionel Messi ba, wanda ke jinya, amma dai Kylian Mbappe da Neymar sun yi fafatawar, kowannensu ya karbi katin gargadi.

Wannan shi ne karo na biyu da PSG wadda ke jan ragamar teburin babbbar gasar tamaula ta Faransa ta barar da maki.

Marseille ce ke biye da PSG da tazarar maki uku tsakani.

Reims, wadda wasa daya kacal ta ci a karawa 10 a Ligue 1 tana ta 14 a kasan teburin kakar bana.