Chelsea na son Rafael Leao, Borussia Dortmund na zawarcin Bellingham

Asalin hoton, Getty Images
Chelsea ta fara tattaunawa domin dauko dan wasan AC Milan Rafael Leao, inda kulub din Serie A din ya amince ya bar dan wasan na Portugal mai shekara 25 kan kudi sama da fam miliyan 63. (Caught Offside)
Arsenal ma ta fara tattaunawa kan dan wasan baya na Faransa William Saliba, 24, kan sabon kwantiragi a daidai lokacin da kungiyar Real Madrid k zawarcin dan wasan. (Athletic - subscription required)
Gunners na gab da kammala tattaunawa kan daukar mai tsaron ragar Sifaniya da ke taka leda a Espanyol, John Garcia mai shekara 24. (Independent)
Dan wasan tsakiya na Sunderland Jobe Bellingham, 19, ka iya bin sahun dan uwan shi Jude mai shekara 21, inda Borussia Dortmund ke shiri kan dan wasan na Ingila ajin 'yan kasa da shekara 21.(Times - subscription required)
Rangers na duba yiwuar sake dauko Steven Gerrard a matsayin manajansu, ko da ya ke ta na kallon Gary O'Neil, Rob Edwards da Russell a matsayin wadanda za su iya dauka idan ciniki bai fada ba akan Gerrard. (Telegraph - subscription required)
Xabi Alonso na son dauko mai tsaron gida na Sifaniya, da ke taka leda a Bournemouth Dean Huijsen, mai shekara 21 zuwa Real Madrid, idan har ya maye gurbin manaja Carlo Ancelotti, a Bernabeu. (Talksport)
Dan wasan Uruguay mai taka leda a Liverpool Darwin Nunez, 25, na daga cikin wadanda Napoli ke son dauka domin karfafa 'yan wasan baya na kungiyar. (Corriere dello Sport - in Italian)
Liverpool za ta tattauna da Luis Diaz, 28, kan sabon kwantiragi a kaka mai uwa, duk da kwantiragin dan wasan na Colombia sai shekarra 2027 zai kare. (TBR Football)
Nottingham Forest ta bi sahun takwarorinta Newcastle da Inter Milan, a zawarcin dan wasan baya na Ingila mai taka leda a kungiyar Liverpool, Jarrell Quansah, 22. (Teamtalk)
Forest ma na son dan wasan tsakiya na Manchester City, James McAtee, sai dai kungiyoyin Tottenham da Bayer Leverkusen, na son dan wasan mai shekara 22. (TBR Football)










