Bellingham ya kafa tarihin cin kwallaye a Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images
Jude Bellingham ya ci kwallo na 14 a bana, bayan Real Madrid ta je ta doke Cadiz 3-0, inda ta koma ta daya a teburin La Liga ranar Asabar.
Yanzu shi ne kan gaba a jerin 'yan wasan Real Madrid da suka fi zura kwallaye da yawa a wasa 15 da fara kakar nan.
Wadanda suka yi irin wannan bajintar a kungiyar a baya, kwallo 13 suka zura a raga ya zuwa wasa na 15, a cikinsu har da Cristiano Ronaldo da Alfredo di Stefano da kuma Pruden.
Dan wasan tawagar Ingila, ya zura kwallo 11 a La Liga a wasa 12 da ukun da ya ci a Champions League, tun bayan komawarsa Spaniya kafin fara kakar nan.
Real ta buga wasa na mako na 14 ranar Asabar da tazarar maki biyu tsakaninta da Girona ta daya, yanzu kungiyar Santiago Bernabeu tana da maki 36.
Sai dai Girona, mai maki 35 za ta kara da Athletic Bilbao ranar Litinin, idan ta ci karawar za ta koma ta daya da tazarar maki biyu tsakaninta da Real.
Rodrygo ne ya ci wa Real kwallo biyu, sannan Bellingham ya kara na uku na 11 a La Liga a kakar nan.









