Ba a tsawaita zaman Vinicius a Real ba, Arsenal na son Zubimendi

Vinicius

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Arsenal ta kusan ɗaukar Martin Zubimendi, Manchester United za ta yi musaya da Rasmus Hojlund domin karɓar Ademola Lookman, Roma da Napoli suna cikin masu son sayen Callum Hudson-Odoi, ba batun tsawaita zaman Vinicius a Real Madrid.

Wakilan Vinicius Jr sun musanta batun cewar ɗan ƙwallon tawagar Brazil ya kusan saka hannu kan kwantiragin ci gaba da taka leda a Real Madrid (Athletic)

Arsenal tana tattaunawa da ɗan wasan tawagar Sifaniya da Real Sociedad, Martin Zubimendi, mai shekara 26, wanda yake da ƙunshin yarjejeniyar sama da fam miliyan 51. kwantiraginsa bai kare ba. (ESPN).

Manchester United na son yin musaya da ɗan wasan tawagar Denmark, Rasmus Hojlund, mai shekara 22 da ɗan wasan Najeriya da Atalanta, Ademola Lookman, mai shekara 27. (Sun ).

Roma da Napoli da wasu ƙungiyoyin Premier League biyu suna son sayen ɗan wasan Nottingham Forest, mai shekara 24, Callum Hudson-Odoi, wanda yarjejeniyarsa za ta kare a karshen kakar baɗi. (Sky Sports)

Newcastle tana son ta biya £30m, kuɗin kunshin yarjejeniyar ɗan wasan tawagar Ingila ta ƴan wasan kasa da shekara 21 mai taka leda a Ipswich, Liam Delap. (Telegraph).

Dan wasan Wolves, Matheus Cunha, mai shekara 25, na son komawa Manchester United, wadda ke fatan sayensa da zarar an kammala kakar bana. (Sky Germany)

Tottenham Hotspur na fatan fara batun mikawa ɗan wasan tawagar Argentina, Cristian Romero mai shekara 26, wanda Real Madrid ke bibiyar wasannin da yake yi. (CaughtOffside).

Atletico Madrid na son sayen ɗan wasan tawagar Uruguay mai taka leda a Tottenham, mai shekara 27, Rodrigo Bentancur. (Times)

Ɗan wasan tawagar Belgian, Albert Sambi Lokonga, mai shekara 25, ya ji rauni, wanda ke buga wasannin aro a Sevilla a kakar nan - na son komawa Arsenal da zarar an kare kakar nan - da ƙyar ne idan Sevilla za ta biya £10.25m domin sayen ɗan wasan.. (Mirror)

Ɗan kwallon tawagar Belgium mai taka leda a Manchester City, Kevin de Bruyne, mai shekara 33, ba zai buga Fifa Club World Cup a watan Yuni ba, domin baya son ya ji raunin da zai hana shi samun sabuwar ƙungiya da zarar an kare kakar nan. (Daily Star).

Tottenham Hotspur tana fatan sayen ɗan wasan tawagar Ingila da Manchester United, Marcus Rashford, mai shekara 27 da zarar an kammala kakar nan. (Football Transfers).